Rundunar Hisbah Ta Ƙara Faɗaɗuwa a Arewa, ana Neman ba su Cikakken Iko
- Rahotanni na nuni da cewa gwamnati ta kaddamar da dakarun Hisba a jihar Sokoto a ranar Alhamis, 22 ga watan Nuwamba
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya buƙaci yan Hisba da su yi aiki tuƙuru da kuma kiyaye dokokin kasa yayin mu'amala da al'umma
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci a ba yan Hisba cikakken iko domin aiki yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da dakarun Hisba a jihar domin fara aiki da kuma taimakawa jami'an tsaro.
Masana na ganin lamarin ya karawa hukumar Hisba karfi a Arewacin Najeriya kuma zai taimaka wajen rage baɗala.
Ma'aikatar addini ta jihar Sokoto ta wallafa a Facebook cewa kwamandan Hisba na jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya halarci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ƙaddamar da yan Hisbah a Sokoto
Rahotanni na nuni da cewa gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya jagoranci kaddamar da yan Hisbah a ranar Alhamis.
Ahmed Aliyu ya yi kira ga yan Hisbah da su kasance wakilai na gari ta inda ba za su yi amfani da aikin wajen muzgunawa al'umma ba.
Gwamnan ya ce yan Hisbah ba kamar yan sanda ba ne saboda haka idan suka kama mutum su mika shi ga jami'an tsaro.
"Muna son tsaftace jihar mu daga haɗala da kuma kawo dabi'u na gari da wasu abubuwan addini, saboda mafi yawan mutanen Sokoto Musulmai ne.
Bayan samar da ofis ofis da motoci, mun daura mutane masu nagarta da za su kula da ayyukan Hisbah."
- Gwamna Ahmed Aliyu
Yan Hisbah: Maganar Sarkin Musulmi
Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Sambo Junaidu da ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya buƙaci a ba yan Hisbah cikakken iko.
Sarkin Musulmi ya ce ta hanyar ba su cikakken iko ne kawai za su iya yin aiki kamar yadda ake tsammani.
Hisbah ta yi sababbin dokoki a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar Hisbah ta haramtawa maza da mata yin hira a cikin mota mai bakin gilashi da zarar karfe 10:00 na dare ta yi a Kano.
Hukumar Hisbah ta kuma haramta duk wani nau'in cacar wasanni a jihar tare da cewa za ta cafke masu ba da hayar gidaje ana aikin badala.
Asali: Legit.ng