Ta Ya Za a Biya?: Dan Siyasa Ya Fadi Kuskuren Tinubu na Karbo Sabon Bashin N1.7trn

Ta Ya Za a Biya?: Dan Siyasa Ya Fadi Kuskuren Tinubu na Karbo Sabon Bashin N1.7trn

  • Hon. Dachung Bagos ya nuna damuwa kan bashin N1.77trn da Shugaba Bola Tinubu zai karbo yana tambayar yadda za a biya
  • Majalisar tarayya ta amince Shugaba Tinubu ya karbo bashin N1.77trn tiriliyan domin cike gibin kasafin kudin 2024 na N9.7trn
  • Sai dai, Bagos, tsohon dan majalisa ya yi gargadin cewa akwai hatsari a tulin bashin da gwamnatin Najeriya ke karbowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon dan majalisar wakilai, Dachung Bagos, ya bayyana damuwarsa kan karuwar bashin da Najeriya ke karbowa, yana tambayar yadda za a iya biya.

Mun ruwaito cewa majalisar tarayya ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na karbo sabon bashin Naira tiriliyan 1.77 ($2.2bn).

Tsohon dan majalisar wakilai ya yi magana kan basussukan da gwamnatin tarayya ke karbowa.
Tsohon dan majalisa ya ce Najeriya na iya shiga matsala saboda yawan bashin da take karbowa. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A zantawarsa da Channels TV, tsohon dan majalisar ya diga ayar tambaya kan yadda gwamnatin tarayyar ke karbo bashi ba ji ba gani.

Kara karanta wannan

'Ba za mu zabi bare ba': Yaron Tinubu ya fara fuskantar kalubale daga matasan Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za ku karbo bashi don cin abinci, biyan kudin makaranta, da biyan komai. Ta yaya za a biyan wadannan basussukan?"

- Bagos ya tambayi gwamnati.

Dan siyasar ya kara da cewa:

"Kullum muna kan hanyar karbo bashi, shin wanne tanadi kuka yi na mayarwa? Mu ba kasar kere-kere ba ce, mu ba kasar fitar da kaya ba ce, ina za mu samu kudin biyan bashin?"

'Najeriya na iya samun matsala" - Bagos

Hon. Bagos ya ce tsarin karbo bashin gwamnati ba zai dore ba, yana mai gargadin cewa sake fasalin haraji na shekara mai zuwa zai kara jefa ’yan kasa a mawuyacin hali.

Tsohon dan majalisar ya ce:

"A yau muna magana ne a kan sake fasalin haraji wanda hakan ke nufin cewa za a kara dorawa 'yan Najeriya haraji mai nauyi a shekara mai zuwa.
"A iya nawa lissafin, kusan kowacce shekara karbo bashinmu na karuwa da kaso 10. Najeriya za ta iya fuskantar matsala idan aka ci gaba da tafiya a haka."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kafa tarihi, ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 3 ga majalisa

Tinubu zai karbo bashin Naira tiriliyan 1.77

Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu na son karbo bashin N1.77trn domin cike gibin kasafin kudin N9.7trn na shekarar 2024.

Tinubu na son karbo wannan bashin ne yayin da bankin CBN ya ce gwamnatin tarayya ta kashe dala biliyan 3.58 wajen biyan basussukan waje a watanni tara na 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.