Nasarawa: Fada Ya Barke Tsakanin Makiyaya da Manoma, An Kashe Mutane da Dama
- Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da rikicin da aka yi tsakanin makiyaya da manoma a yankin Dogon Dutse
- Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Umar Nadada ya ce an kashe mutane uku a rikicin yayin da rundunar ke gudanar da bincike
- CP Nadada ya ce rundunar ta hada kai da mutanen yankin domin kamo wadanda suka tayar da tarzoma tare da hukunta su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Nasarawa - Mutane uku ne suka mutu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Dogon Duste da ke jihar Nasarawa.
An rahoto cewa garin da aka yi arangamar ya na nan tsakanin kananan hukumomin Nasarawa da Toto a jihar.
Makiya da manoma sun yi arangama
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, CP Umar Nadada, ya bayyana faruwar lamarin a garin Lafia ranar Alhamis, a cewar rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Shugaban ofishin ‘yan sanda (DPO) ya samu rahoton cewa rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba da misalin karfe 4:30 na yamma.
“Bayan isa wajen, an gano cewa an kashe mutane biyu a cikin wata gona, yayin da hudu suka samu raunuka, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.”
- A cewar kwamishinan.
Mutane uku sun mutu a rikicin
Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sandan ta kuma sake gano wata gawa a cikin daji a yayin gudanar da bincike, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa uku.
Nadada ya kara da cewa an dawo da zaman lafiya a cikin yankin yayin da rundunar 'yan sandan ke ci gaba da bincike domin sanin tushen lamarin.
Rundunar ‘yan sanda ta hada kai da mutanen garin domin kamo wadanda suka haddasa rikicin tare da tabbatar da sun fuskanci doka.
An kashe mutane uku a Jigawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa rikicin manoma da makiyaya ya jawo an kashe mutane uku a yankin gandun dajin Baranda da ke jihar Jigawa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawal Shiisu ya shaidawa Legit Hausa cewa sabanin fahimta tsakanin makiyaya da manoman ne ya jawo rikicin.
Asali: Legit.ng