'Akwai Haɗari,' Atiku Ya Magantu da Jin Najeriya Ta Kafa Mummunan Tarihin Bashi
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nuna bacin rai kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke ciwo bashi
- Atiku Abubakar ya ce abin takaici ne a cigaba da ciwo bashi bayan Najeriya ta zamo kasa ta uku da ta fi tarin bashi a fadin duniya
- A cewar Atiku, a lokacin Olusegun Obasanjo aka rage mafi yawan bashin da ake bin Najeriya amma yanzu an koma gidan jiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Atiku Abubakar ya yi magana yayin da Bola Ahmed Tinubu ya samu amincewar ciwo bashin Naira tiriliyan 1.7.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce abin takaici ne yadda ake ciwo bashi kuma ake karkatar da shi a Najeriya.
Atiku Abubakar ya wallafa a Facebook cewa a yanzu haka Najeriya ta kafa mummunan tarihi a bangaren cin bashi a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya koka kan tarin bashin Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce akwai damuwa kan yadda Tinubu ke ciwo bashi.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa Atiku ya ce abin takaici ne yadda Najeriya ta kafa mummunan tarihin zama ta uku wajen cin bashi a duniya duk da tsamo kasar da aka yi a lokacin Obasanjo.
Ya kara bayyana cewa lokaci ya yi da za a yi taka tsantsan wajen cin bashin da ba ya amfani ga yan Najeriya.
"Najeriya na kara fadawa cikin tarin bashi. Tinubu ya ce suna tattara haraji sosai amma kuma kullum suna kara ciwo bashi.
Lallai akwai abin da suke boyewa yan kasa a kan wannan lamarin, duk da cewa tukin tsaye da suke ma zai iya hana lamura tafiya daidai.
Bashin da Tinubi ke ciyowa zai nakasa yan Najeriya tare da jefa kasar cikin matsalar tattali."
- Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya ce karin takaici shi ne yadda ake ciwo bashi sosai kuma kwalliya bata biyan kudin sabulu.
A cewar Atiku Abubakar, binciken cibiyar Budgit ya nuna cewa akwai alamar tambaya a kan yadda ka kashe kasafin kudin 2024.
ACF ta yi kira ga Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa ta yi kira ga Bola Tinubu kan buƙatar sauya tsare tsarensa.
Shugaban ACF, Mamman Mike Osuman ya ce ba yadda za a yi a kawo tsarin da ke kara talauta mutane kuma a ce za a cigaba.
Asali: Legit.ng