"Babu Ruwan Tinubu": Kwankwaso Ya ba ACF Shawara kan Matsalolin Arewa

"Babu Ruwan Tinubu": Kwankwaso Ya ba ACF Shawara kan Matsalolin Arewa

  • Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi martani kan batun da ƙungiyar ACF ta yi na cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa
  • Jigon na.jam'iyyar APC a jihar Kano ya bayyana cewa bai kamata ƙungiyar ta riƙa sukar gwamnatin Bola Tinubu ba
  • Ya shawarci ƙungiyar da ta maida hankali wajen magance ɗimbin matsalolin da suka daɗe suna addabar yankin Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jigo a jam’iyyar APC a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi kira da babbar murya ga ƙungiyar ACF kan sukar gwamnatin Bola Tinubu.

Musa Kwankwaso ya buƙaci ƙungiyar ACF da ta maida hankali wajen magance ɗimbin matsalolin da Arewa ke fuskanta maimakon sukar gwamnatin Tinubu kan abubuwan siyasa.

Kwankwaso ya ba ACF shawara
Kwankwaso ya bukaci ACF ta daina sukar Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Musa Iliyasu Kwankwaso
Asali: Facebook

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan zargin da ACF ta yi na cewa an yi watsi da yankin Arewa, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

An samu rabuwar kai a APC kan zargin sakataren gwamnatin Tinubu da ƙabilanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta ACF ta caccaki gwamnatin tarayya inda ta yi zargin cewa an yi watsi da yankin Arewacin Najeriya.

Wacce shawara Kwankwaso ya ba ACF

Kwankwaso ya shawarci ƙungiyar ACF da ta shirya taron tattaunawa wanda zai haɗa shugabannin addini, na gargajiya da na siyasa a yankin, domin magance ɗimbin matsalolin da ke addabar Arewa.

"Ya kamata mu Arewa mu zauna mu duba yadda za mu magance matsalolin da ke addabar mu, mu daina zarge-zarge na ɗora laifi ga Shugaba Tinubu."
"Mu ƴan Arewa mu saurara mu yi aiki da abin da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya ce ba ma son kanmu. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka kasa haɗa kai domin fuskantar ƙalubalen da ke addabar yankin."

- Musa Iliyasu Kwankwaso

Kwankwaso ƙara da cewa matsalolin da ake fuskanta a yanzu, musamman Arewa, ba gwamnatin Tinubu ta samar da su ba, an gada ne daga gwamnatocin baya.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya cika baki kan binciken da EFCC ke yi masa

Kwankwaso ya ba ƴan Arewa shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jagora a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya jaddada cewa ya fi kyau Arewa ta goyi bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2027 domin mulki ya koma yankin a 2031.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma jaddada bukatar ƴan siyasa masu kishin kasa su yi watsi da yunƙurin da wasu ke yi na ɓata gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng