'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Matashin Lauya a Jihar Benue
- Ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Benue bayan sun farmaki wani matashin lauya har gidansa a daren ranar Laraba
- Lauyan wanda ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam ne ya rasa ransa a harin da ƴan bindigan suka kai masa
- Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta tabbatar da kashe inda ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Wasu ƴan bindiga sun harbe wani matashin lauya, Barista Mike Ofikwu a garin Otukpo na jihar Benue.
Mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindiga sun harbe lauyan wanda ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam ne a daren Laraba a kusa da gidansa da ke kan titin Otukpa a Otukpo.
Yadda ƴan bindiga suka kashe lauyan
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga biyu ne suka kai masa hari a lokacin da yake ƙoƙarin shiga gidansa inda suka buɗe masa wuta, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Punch ta rahoto cewa an garzaya da shi wani asibiti da ke kusa inda aka tabbatar da rasuwarsa bayan sun isa.
"Kamar irin abin nan ne da ake gani a cikin fina-finai. Dawowarsa kenan yana jiran ƙofar shiga gidan ta buɗe masa domin ya wuce."
"Kwatsam kawai sai wasu mutane su biyu da ke kan abin hawa suka zo kusa da shi suka buɗe masa wuta sannan suka guda."
- Wata majiya
Ƙungiyar lauyoyi da mazauna garin Otukpo sun shiga jimamin rashin matashin lauyan.
An ji ta bakin rundunar ƴan sanda?
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar harin na ƴan bindiga.
"Eh lamarin ya auku kuma ana ci gaba da gudanar da bincike. Ina miƙa ta’aziyya ga iyalansa da abokansa tare da tabbatar musu da cewa za a yi adalci."
- SP Catherine Anene
Sojoji sun cafke mai taimakon ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar birged ta 6 sun cafke wani Alhaji da ake zargin yana taimakawa ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba.
Sojoji sun damke mutumin ne yayin da suka kai samamen tsaftace yankin daga miyagu musamman saboda zuwan lokacin kaka da mutane ke kawo amfanin gona gida.
Asali: Legit.ng