Majalisar Dattawa Ta Amince Bola Tinubu Ya Karɓo Bashin Sama da Naira Tiriliyan 1.7
- Majalisar dattawan Najeriya ta amince shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓo baahin Naira tiriliyan 1.76 daga waje
- A zaman ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, majalisar ta amince da bukatar ne bayan ta karɓi rahoton kwamitin kula da basussukan gida da na waje
- Tun farko Shugaban Ƙasa Tinubu ya yi bayanin cewa zai karbo bashin ne domin cike gibin kasafin kudin 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta sahalewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara runtumo rancen kuɗi sama da Naira tiriliyan 1.7
A zaman yau Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, 2024, majalisar ta amince Tinubu ya karɓo rancen N1,767,610,321,779.00 a kuɗin Najeriya.
Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo bashi
The Nation ta ruwaito cewa sanatoci sun amince da bukatar ne bayan nazari kan rahoton kwamitin majalisar dattijai mai kula da basussukan gida da waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin basussukan da ake bin Najeriya a gida da waje, Sanata Aliyu Wamakko ne ya gabatar da rahoton.
Tun farko dai shugaban kasa Tinubu ya tura bukatar neman izinin majalisar na sake ciyo bashin sama da Naira tiriliyan 1.7 domin cike giɓin kasafin kudin 2024.
Shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta saƙon Tinubu a zaman ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba, 2024.
Abin da Bola Tinubu zai yi da kudin
A cikin wasikar, Tinubu ya yi bayanin cewa za a yi amfani da wannan bashin da zai karɓo wajen aiwatar da kasafin kudin 2024.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa bukatar ta yi daidai tanadin sashe na 21 (1) da na 27 (1) na ofishin kula da basussuka, kuma majalisar zartaswa FEC ta amince.
Bayan nazari kan rahoton da Wamakko ya gabatar a zaman yau Alhamis, majalisar dattawan ta amince Tinubu ya ciyi bashin, rahoton Daily Trust.
Bola Tinubu ya aika sako majalisa
Kuna da labarin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunayen mutum uku da ya naɗa a matsayin kwamishinonin zaɓe watau REC ga majalisar dattawa.
Sababbin kwamishinonin zaɓen sun haɗa da Abdulrazak Yusuf wanda zai kuƙa da shiyyar Arewa maso Yamma da Feyijimi Ibiyemi na Ondo.
Asali: Legit.ng