Majalisa: Ana Shirin Sauya Wurare 161 a Kundin Mulkin Najeriya na 1999

Majalisa: Ana Shirin Sauya Wurare 161 a Kundin Mulkin Najeriya na 1999

  • Majalisar dokokin Najeriya ta yi bayani kan kokarin da ta fara na sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999
  • Mataimakin shugaban majalisar dokoki, Hon. Benjamin Kalu ne ya yi bayani yayin ganawa da gwamnonin jihohi a ranar Laraba
  • An ruwaito cewa Hon. Benjamin Kalu ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da za a sauya a kundin tsarin mulkin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shirye shiryen sauya fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 sun fara yin nisa.

Majalisa
Za a sauya wurare a 161 a kundin tsarin mulki. Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban majalisar dokokin Najeriya, Hon. Benjamin Kalu ya bayyanawa gwamnonin jihohi halin da ake ciki a kan aikin.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Benjamin Kalu ya ce ana shirin sauya wurare sama da 150 a kundin tsarin mulkin.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi halin da tattalin arziki ke ciki bayan fara mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsarin mulki: Za a sauya wurare 161

Majalisar dokokin Najeriya ta bayyana cewa ana shirin sauya abubuwa 161 a kudin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Shugaban kwamitin sauya tsarin mulki kuma mataimakin shugaban majalisa, Hon. Benjamin Kalu ne ya bayyana haka.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Hon. Kalu ya bayyanawa gwamnonin Najeriya kokarin da suke yi na ganin an sauya tsarin mulkin a kan lokaci.

"Za mu cigaba da nazari kan korafi 161 da muka karba a kan sauya fasalin kundin tsarin mulkin 1999.
Za mu rika ganawa da tattaunawa a kai a kai domin muna so sauyin da za mu yi ya fi na baya kyau."

- Hon. Benjamin Kalu

Daga cikin abubuwan da ake hasashen majalisar za ta mayar da hankali a kai akwai yan sandan jihohi, zabe daga ƙetare, shari'a a kan zabe da sauransu.

Ana kyautata zaton cewa zuwa karshen watan Disambar shekarar 2025 majalisar wakilai za ta kammala aikin.

Kara karanta wannan

Tinubu zai karbo sabon bashin Naira tiriliyan 1.7, ya fadawa majalisa dalilinsa

Ana shirin kawo sabuwar dokar zabe

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta yi karatu na biyu ga kudirin ba yan Najeriya damar zabe daga ƙetare.

Idan kudirin ya samu tabbatuwa, yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje za su rika kada kuri'a yayin zabuka kamar wadanda ke cikin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng