Gwamna Ya Ba da Umarnin Rufe Makarantu Saboda Mutuwar Sanata, Bayanai Sun Fito

Gwamna Ya Ba da Umarnin Rufe Makarantu Saboda Mutuwar Sanata, Bayanai Sun Fito

  • Gwamna Soludo na jihar Anambra ya ba da hutun makarantu a yankin Nnewi yayin da ake shirin jana'izar Sanata Ifenyi Uba
  • Charles Soludo ya umarci shugabannin makarantun yankin su ba ɗalibai hutu daga nan zuwa ranar Talatar mako mai zuwa
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da mutane ke fargaba kan barazanar da miyagu suka yi na kawo cikas idan ba yi abin da suke so ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Solido ya ba da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da ke Nnewi zuwa makon gobe.

Gwamna Soludo ya ɗauki wannan matakin ne domin kaucewa yiwuwar tada zaune tsaye a lokacin bukukuwan jana'izar marigayi Sanata Ifeanyi Ubah.

Gwamna Soludo.
Gwamna Soludo ya ba da hutun makarantu saboda jana'zar Sanata Ifeanyi Ubah Hoto: Charles Chikwuma Soludo
Asali: Twitter

Dalilin gwamna ba bada hutun makarantu

Rahoton The Nation ya nuna cewa ƴan bindiga sun yi barazanar tada hankula idan har aka yi jana'izar Ubah ba tare da an warware wasu batutuwa ba.

Kara karanta wannan

'Tsaro a makarantu': Tinubu zai kashe N112bn a gagarumin aiki da ya tattago

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fargaba kan wannan barazana ta karu a zukatan jama'a a daren Laraba yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a Nnewi, suka kashe mutane tare da kona mota.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 7:30 na dare, ya haifar da firgici, inda mazauna yankin suka tsere domin tsira da rayukansu.

Yayin da ake shirin binne gawar Sanata Ubah ranar Juma’a a kauyen Umuanuka, Otolo Nnewi, gwamnatin Anambra ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis.

Gwamna ya aika saƙo ga iyayen yara

Gwamnatin ta umurci dukkan shugabannin makarantun da ke yankin Nnewi su ba ɗalibai hutu daga nan zuwa ranar Talata mako mai zuwa. 

Haka kuma an shawarci iyayen yaran da ke karatu a makarantun jeka ka dawo da su rike ƴaƴansu a gida, ka da su bari su fito domin gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.

"Barka da safiya iyayen yara, ku sani wannan sakon daga bakin kwamishinan ilimi ya fito, kada ku bar yaranku su taho makaranta har sai ranar Talata ta makon gobe."

Kara karanta wannan

Kwamitin binciken gobarar tankar fetur a Jigawa ya mika rahotonsa ga gwamnati

Shettima ya yabawa Marigayi Ifeanyi Ubah

Kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima ya yaba da halin kirki na marigayi Sanata Ifeanyi Ubah.

Kashim Shettima ya bayyana cewa marigayin ya taɓa taimakon jihar Borno bayan wani hari da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262