Duk da Yarjejeniya da Najeriya, Matatar Dangote za Ta Sayo Danyen Mai daga Amurka

Duk da Yarjejeniya da Najeriya, Matatar Dangote za Ta Sayo Danyen Mai daga Amurka

  • Matatar Dangote ta na jiran danyen mai daga kasar waje duk da kokarin gwamnatin Najeriya ya sayar mata kaya da sauki
  • A baya ne gwamnatin kasar nan da Dangote su ka cimma matsaya kan sayarwa matatar danyen fetur da Naira a maimakon Dala
  • Sai dai an samu rahoton za a shigowa da Dangote da danyen mai akalla ganga miliyan biyu a wata mai kamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar LagosMatatar Dangote ta bayyana yiwuwar cigaba da sayo danyen man fetur daga kasar Amurka a kokarinta kara yawan fetur da ta ke tacewa.

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin Dangote ya dakatar da sayo danyen man daga kasashen ketare a tsawon watanni uku.

Kara karanta wannan

Kano: Malamar da ta haura shekaru 20 ta na haura rafi don da'awa ta fara samun tagomashi

Dangote
Matatar Dangote za ta sayo danyen fetur daga Amurka Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Kafar Bloomberg ta ruwaito cewa matatar ta mayar da hankali ne a wajen sayen danyen man da ta ke bukata a cikin gida Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote zai dauko danyen mai daga Amurka

Jaridar Punch ta wallafa cewa matatar Dangote ta na jiran ganga miliyan biyu na danyen man fetur daga kamfanin Chevron Corp a watan gobe.

Wannan na nuna cewa wannan kamar manuniya ce na cewa shirin gwamnatin tarayya na sayarwa matatar danyen mai bai yi tasirin da ake zato ba.

Yadda matatar Dangote ke samun danyen mai

A farkon shekarar nan ne matatar Dangote ta rika sayen manyan tankokin danyen mai daga kasar Amurka akalla guda biyu a wata, hadi da wanda ta ke samu a Najeriya.

Amma matatar ta rage shigo da man daga ketare a wuraren watan Agusta bayan ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya na sayen danyen man kasar nan da Naira a maimakon Dala.

Kara karanta wannan

Kwamitin binciken gobarar tankar fetur a Jigawa ya mika rahotonsa ga gwamnati

Matatar Dangote za ta samar da fetur

A baya mun ruwaito cewa matatar Dangote da kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) sun cimma matsaya kan samar da fetur lita miliyan 240 a duk wata don sayarwa jama'a.

Wannan na zuwa ne bayan dillalan fetur din sun yi alkawarin kasar nan za ta samu saukin farashin litar fetur da zarar matatar Dangote ta fara sayar masu man kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.