An Samu Bayanai wajen Musayar Wuta Tsakanin 'Yan Sanda da 'Yan Banga

An Samu Bayanai wajen Musayar Wuta Tsakanin 'Yan Sanda da 'Yan Banga

  • An samu kuskuren rashin fahimta tsakanin jami'an ƴan sanda da ƴan banga a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra
  • Kuskuren ya jawo jami'an tsaron sun buɗewa junansu wuta bayan sun yi tunanin cewa suna fafatawa ne da ƴan bindigan ƙungiyar IPOB
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana an garzaya da wasu mutum biyu zuwa asibiti bayan sun samu rauni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - An yi ɗauki ba daɗi a tsakanin ƴan banga da jami'an ƴan sanda a jihar Anambra.

An yi musayar wutan ne bayan jami'an tsaron sun yi kuskuren cewa suna fafatawa ne da ƴan bindigan ƙungiyar IPOB a ranar Laraba.

'Yan sanda sun fafata da 'yan banga a Anambra
'Yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan banga bisa kuskure a Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan sanda sun fafata da ƴan banga

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare a mahaɗar Izuchukwu da ke kan titin Nnobi-Nnewi a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wurin da lamarin ya faru na kusa da garin Otolo Nnewi, mahaifar marigayi Sanata Ifeanyi Ubah, wanda za a yi jana'izarsa ranar Juma'a.

Wasu mazauna garin sun ce sun yi tunanin ƴan bindigan IPOB ne waɗanda suka yi barazanar hana binne Sanatan suka yi musayar wuta da jami’an ƴan sandan.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin da lamarin ya faru a gaban idonsa, amma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ana farbagar mutuwar wasu mutane biyu da harsashi ya same su, rahoton Punch ya tabbatar.

Ƴan sanda sun yi ƙarin haske

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin

Tochukwu Ikenga ya ce ƴan bangan sun yi kuskuren ɗaukar ƴan sandan a matsayin abokan gaba sannan suka buɗe musu wuta.

Ya bayyana cewa mutane biyu sun samu rauni sakamakon arangamar, kuma an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Ƴan bindiga sun farmaki ƴan sanda

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun farmaki sansanin sojoji, sun hallaka jami'ai masu yawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe wasu jami'an ƴan sanda da ba a tantance adadinsu ba a ƙaramar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

Majiyoyi sun bayyana cewa wurin da aka kai harin ya koma ba kowa yayin da mutane suka yi ta tururuwar guduwa domin tsira da rayukansu saboda fargaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng