Gwamna Ya Shiga Matsala kan Rusa Shaguna, Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci
- Bayan shekaru kusan 10, wani mutumi da aka rusa shagunansa a jihar Enugu ya samu nasara a babbar kotun jihar
- Kotun ta umarci gwamnatin Enugu karkashin jagorancin Gwamna Peter Mbah ta biya mutumin diyyar N55m bisa rusa shagunansa ba bisa ka'ida ba
- A ranar 24 ga watan Yuli, 2015, mutumin mai suna Chinedu Onyebuchi ya kai ƙarar hukumar raya babban birnin Enugu kan rusa shagunan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu - Babbar kotun jiha ta umarci gwamnatin Enugu ta biya wani mutumi mai suna Chinedu Onyebuchi, kudi N55m kan rusa masa shaguna.
Kotun ta ba umarci hukumar raya babban birnin jihar Enugu ta biya mutumin waɗannan kuɗaɗen ne sakamakon rusa masa shaguna ba bisa ka'ida ba.
Premium Times ta ce Onyebuchi, ya kai karar hukumar ne a ranar 24 ga watan Yulin 2015, kimanin shekaru 10 da suka wuce bayan ta rushe shagunansa guda shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan kasuwa ya kai karar gwamna kotu
Tun farko ya roki kotu ta bayyana cewa rusa shagunanaa da hukumar raya birni ta yi ya sabawa doka, ya saɓa kundin tsarin mulki, kuma bai dace ba.
Mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa sai da ya samu takardar sahalewa daga hukumar kafin ya gina shagunansa.
Mista Onyebuchi ya kuma nemi kotun ta hana hukumar ko jami’ansu cin zarafi ko kawo masa cikas a wurin ginin, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Ɗan kasuwar ya roki kotu da ta umurci hukumar da ta biya shi Naira miliyan 30 na rusa masa ginin shaguna da Naira miliyan 50 a matsayin diyya.
Wane hukunci kotu ta yanke?
Da yake hukunci ranar Laraba, mai shari'a Kenneth Okpe ya ce kotu ta gamsu hukumar ta yi gaban kanta ta rusawa mutumin shagunsa ba bisa ƙa'ida ba.
"Ina umartar hukumar da ake ƙara ta biya wanda ya kawo ƙara kudi Naira Miliyan 30 a matsayin diyyar ginin shaguna shida da kayyakin ciki.
"Sannan kuma ta biya ƙarin N25m a matsayin diyyar gaba ɗaya ɓarnar da aka yi wa wanda ke ƙara," in ji Alkalin.
Gwamna Mbah zai fara biyan albashin N80,000
A wani labarin, an ji cewa Gwamna Peter Ndabuisi Mbah ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 a kowane wata ga ma'aikatan jihar Enugu.
Gwamnan ya bayyana cewa amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin na daga cikin alƙawarin da ya ɗauka a lokacin kamfe.
Asali: Legit.ng