Tinubu Ya Samo Mafita kan Yaki da Ta'addanci a Afrika
- Shugaban Najeriya ya gano hanyar da kasashen Afrika za su bi wajen kakkabe matsalar rashin tsaro a shiyyar
- Bola Ahmed Tinubu ya fadi haka ne lokacin da ya kaddamar da gasar dakarun sojojin Afrika a Abuja
- Ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta gagari wata kasa ta kawo karshensa ita kadai, dole sai an hada kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed ya fadi hanyar da za a bi wajen magance matsalar ta’addanci da ayyukan miyagun mutane a nahiyar Afrika.
Shugaba Tinubu ya fadi haka ne a lokacin da ya bude gasar dakarun sojoji na nahiyar Afrika da ya gudana a babban birnin tarayya, Abuja.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa Tinubu ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima, inda ya mika bukatar kasar nan ga sauran kasashen Afrika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya nemi hadin kan Afrika kan tsaro
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban Najeriya ya fadi hanyar da kasashen nahiyar Afrika za su bi wajen magance matsalar rashin tsaro da ta addabe su.
Bola Tinubu ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen su yi aiki tare domin tabbatar da an magance tsagerun da ke hana zaune tsaye a nahiyar baki daya.
Rashin tsaro: Tinubu ya fadi muhimmancin hadin kai
Shugaban kasar nan ya nanata cewa babu wata kasa da za ta iya kawo karshen ta’addancin da ta ke fuskanta ba tare da taimakon makwabtan kasashe ba.
Shugaba Bola Tinubu y ace;
“A yau, mun kara tabatar da alkawarin cewa za mu iya cimma manufar da mu ka sa a gaba idan mun yi aiki tare – ba wai kawai a matsayin makwabta ba, amma a matsayin masu kare juna da sadaukar da kai da jajircewa.”
Tinubu ya dauko aikin samar da tsaro
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta bayyana sabon shirinta na tabbatar da an samar da tsaron rayukan dalibai da ke karatu a makarantun da ke jihohi daban-daban.
Ministar harkokin mata, Imaan Suleiman-Ibrahim ta bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin sabon shirinta za ta kashe N112bn domin tabbatar da tsaron makaranta daga miyagu.
Asali: Legit.ng