Yaki da Badala: Hisbah Ta Lalata Barasar Makudan Kudi a Jihar Yobe
- Hukumar Hisbah a jihar Yobe ta lalata kwalaben barasa da ta ƙwace a yayin wani aikin sintiri da ta fita
- An lalata kwalaben barasar sama da 170 waɗanda kuɗinsu ya kai N450,000 a garin Gashua, hedkwatar ƙaramar hukumar Bade ta jihar
- Shugaban ƙaramar hukumar wanda ya jagoranci aikin lalata barasar ya ce za su sanya ƙafar wando ɗaya da masu sayarwa da sha a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Hukumar Hisbah ta jihar Yobe ta lalata kwalaben barasa sama da 170 waɗanda kuɗinsu ya kai N450,000.
An ƙwace kwalaben ne a ɗaya daga cikin otal ɗin da ke garin Gashua, hedkwatar ƙaramar hukumar Bade.
Hisbah ta lalata barasa a Yobe
Shugaban ƙaramar hukumar Bade, Ibrahim Babagana Yurema, wanda ya jagoranci lalata barasar, ya ce za su fatattaki masu sayar da barasa da masu saya a yankin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an ƙwace kwalaben ne a yayin wani sintiri da hukumar Hisbah ta yi a ɗaya daga cikin fitattun otal da ke Gashua, inda sun damu matuƙa da shaye-shaye a tsakanin matasan.
Ibrahim Babagana Yurema ya ce shan barasa da sauran abubuwan sa maye da ke gurɓata tunanin mutum haramun ne a addinin Musulunci, yana mai jaddada cewa za su ci gaba da yaƙi da wannan mummunar ɗabi’a.
Kotu ta tsare mai sayar da barasa
Kwamandan hukumar Hisbah na shiyyar Yobe ta Arewa, Malam Isah Ibrahim, ya ce kotun shari’ar Musulunci a jihar ta samu mai sayar da barasan da laifi sannan ta tura shi gidan kaso.
Ya kuma ƙara da cewa kotun ta kuma umarci hukumar Hisbah da ta lalata barasar da aka ƙwace.
Hisbah ta ƙwace barasa a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta ƙwace kimanin katan 142 na barasa da aka shirya kaiwa ƙaramar hukumar Daura.
Kwamandan Hisbah na jihar, Dakta Aminu Usman ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya.
Asali: Legit.ng