Dalibai Sama da 10 Sun Jikkata da Faɗa Ya Barke Tsakanin Makarantu 2 a Arewa

Dalibai Sama da 10 Sun Jikkata da Faɗa Ya Barke Tsakanin Makarantu 2 a Arewa

  • Ɗaliban makarantun gwamnati biyu a yankin Adeta a Ilorin, babban birnin jihar Kwara sun kaure da faɗa kan wata jiƙaƙƙiyar gaba
  • Mazauna yankin sun ce akalla ɗalibai 10 ne suka ji raunuka a faɗan wanda ya afku ranar Litinin da misalin karfe 11 na safe
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce dakarunta sun kama wasu daga ciki a lokacin da suka kai ɗauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara - Ɗalibai da dama sun jikkata sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin daliban wasu makarantun sakandare biyu a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Lamarin dai ya afku ne ranar Litinin da ta gabata kuma sama da ɗalibai 10 sun samu raunuka daban-daban.

Taswirar jihar Kwara.
Daliban makarantu 2 sun yi arangama a babban birnin jihar Kwara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ganau ya shaidawa Daily Trust cewa faɗan ya kaure tsakanin ɗaliban makarantun biyu da misalin ƙarfe 11:00 na safe a yankin Adeta a Ilorin.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ɓarke kan harbin hadimin gwamna a ofishin ƴan sanda, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗalibai sun jikkata a faɗan makarantu 2

Mutumin ya ce ɗaliban makarantar Government High School da na makarantar sakandiren jeka ka dawo ta gwamnati ne suka yi faɗa da juna kan wata rashin jituwa.

"Sama da dalibai 10 ne suka jikkata a rikicin da ya jefa mutane cikin tashin hankali. Rikicin ya fara ne makonni biyu da suka wuce, ana ganin abin da ya faru ramuwa ce," in ji shi.

Wasu dai na ganin abin da ya faru yana da alaƙa da ƙungiyoyin asiri da kuma faɗan iko.

Da aka tuntubi sakataren yada labarai a ma’aikatar ilimi ta jihar, Peter Amogbonjaye, ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin.

Wane mataki aka ɗauka kan ɗaliban?

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi (DSP), ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ƴan sanda sun kama wasu da ake zargi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mace 'yar fashi da makami da wasu matasa a Bauchi

Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin fadan daliban makarantun guda biyu.

Dalibi ya kafa tarihi a Jami'ar Ilorin

A wani rahoton kun ji cewa wani matashi da ya karanci darasin lissafi a Jami'ar Ilorin da ke Kwara ya samu sakamako mai daraja ta ɗaya da lambar yabo

Ɗalibin ya wallafa sakamakon da ya samu a soshiyal midiya bayan ya kammala karatun digirin farko a wannan makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262