Kwana 1 da Sakon Tinubu, Gwamnoni Sun Shiga Ganawar Gaggawa, an Samu Bayanai
- Kwana daya bayan Tinubu ya turawa shugabannin Arewa sako, kungiyar gwamnonin Najeriya ta shiga ganawar gaggawa
- Gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara za su tattauna matsaloli da dama
- Daga cikin abubuwan da ake sa ran za su tattauna akwai asusun rarar danyen mai (ECA) da harajin man fetur da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnonin Najeriya sun shiga ganawar gaggawa a daren yau Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024.
Gwamnonin ƙarƙashin kungiyar NGF sun shiga ganawar domin tattauna wasu matsalolin da suka shafi Najeriya.
Gwamnonin Najeriya sun shiga wata ganawa a Abuja
Leadership ta ce gwamnonin suna ganawar karkashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin sun fara zaman da misalin karfe 8:30 na daren yau Laraba a birnin Abuja.
Ana sa ran za su tattauna batutuwa da suka shafi sarakunan gargajiya da asusun rarar danyen mai da kuma haraji musamman ta bangaren man fetur.
Batutuwa da za su dauki hankali a ganawar
Har ila yau, za a gabatar da bayani ga gwamnonin kan bikin zuba hannun jari da Najeriya za ta halarta a kasar Morocco.
Ana hasashen taron da Najeriya za ta halarta zai inganta tattalin arziki da kuma zuba hannu jari a kasar da zai kawo sauyi a yanayin da ake ciki.
Daga bisani, Ministan ilimi, Tunde Alausa zai yi bayani kan tsare-tsaren gwamnati domin inganta harkar ilimi a Najeriya.
Mataimakin shugaban Majalisar Dokoki, Hon. Benjamin Kalu shi ma zai yiwa gwamnonin karin haske kan gyaran fuska da ake kokarin yi a kundin tsarin mulki.
An gano masu laifi kan matsalolin Arewa
Kun ji cewa wasu na zargin Shugaba Bola Tinubu kan matsalolin Arewa, kungiyar ACF ta yi martani mai tsauri kan matsalolin yankin.
Shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum, Mamman Mike Osuman ya ce matsalolin Arewa laifin shugabanninta ne.
Osuman ya ce ba za su daurawa Tinubu laifi ba kan abubuwan da ke faruwa duk da tsare-tsarensa ba su dace da yankin ba.
Asali: Legit.ng