Gwamna Ya Yi Zazzaga, Ya Sallami Ma'aikata a Manyan Makarantu da Asibitoci

Gwamna Ya Yi Zazzaga, Ya Sallami Ma'aikata a Manyan Makarantu da Asibitoci

  • Gwamna Monday Okpebholo ya rusa majalisar gudanarwa na manyan makarantun da ke ƙarƙashin gwamnatin Edo
  • Sakataren watsa labaran gwamnan, Fred Itua ya ce Okpebholo ya kuma amince da korar shugabannin manyan asibitoci biyu nan take
  • Duk da ba a bayyana dalilin ɗaukar wannan mataki ba amma ana ganin ba zai rasa alaƙa da canjin gwamnatin da aka samu a jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya rusa majalisar gudanarwa ta jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma.

Gwamnan ya kuma rusa majalisun gudanarwa na dukkan manyan makarantun gaba da sakandire da ke ƙarƙashin gwamnatin jihar Edo.

Gwamna Monday Okpebholo.
Gwamnan Edo ya rusa majalusun gudanarwa na manyan makarantun jihar Hoto: @EdoStateGovt
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan Edo, Fred Itua, ya fitar ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ɓarke kan harbin hadimin gwamna a ofishin ƴan sanda, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnan ya kuma sallami jagororin asibitin kwararru na Edo da kuma asibitin Stella Obasanjo da ke birnin Benin daga aiki nan take.

Gwamnan Edo ya kori shugabannin makarantu

A rahoton Tribune, Fred Itua ya ce:

"Gwamnan Edo, Mai girma Sanata Monday Okpebolo ya amince da rusa majalisum gudanarwa na dukkan manyan makarantun jihar ba tare da bata lokaci ba.
"Saboda haka ana umartar dukkan waɗanda wannan mataki ya shafa su miƙa kayayyakin gwamnati da ke hannunsu ga shugabannin makarantu."
"Haka nan kuma Gwamna Okpebholo ya kori shugabannin gudanarwa na asibitin kwararru na jihar Edo da asibitin Stella Obasanjo da ke Benin ba tare da ɓata lokaci ba."

Meyasa gwamnan ya ɗauki matakin kora?

Hadimin gwamnan ya ƙara da cewa gwamnati na sa ran ma'aikatan waɗannan asibitoci da matakin ya shafa za su miƙa kayayyakin da ke hannunsu ga na ƙasa da su.

Sai dai sakataren watsa labaran gwamnan bai bayyana dalilin korar waɗannan ma'aikata ba amma ana ganin ba zai rasa nasaba da canjin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Gwamma ya kere N70,000, ya faɗi sabon albashin da zai fara biyan ma'aikata

Gwamna Okpebholo ya yi naɗe-naɗe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya naɗa ƙarin kwamishina ɗaya da shugabannin wasu hukumomin gwamnati

Naɗe-naɗen na kunshe a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin Edo, Umar Ikhilor.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262