'Yan Sanda da Soja Sun Kaure da Faɗa, An Harbe Wani Bawan Allah Har Lahira

'Yan Sanda da Soja Sun Kaure da Faɗa, An Harbe Wani Bawan Allah Har Lahira

  • Ƴan sanda sun ja daga da wani soja a jihar Ebonyi yayin da ya masu gardama a bakin aikinsu na binciken ababen hawa
  • Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya yi sanadin harbe wani mutum da ya zo wucewa tare da jikkata wasu mutum uku
  • Kwamishiniyar ƴan sanda ta jihar Ebonyi tace yanzu haka ƴan sandan da sojan suna tsare kuma za a gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Wasu ƴan sanda da soja guda ɗaya sun kaure da faɗa a jihar Ebonyi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani ɗan kallo da ke tsaye a gefe.

An ruwaito cewa Lamarin ya faru ne bayan wata takaddama ta shiga tsakanin ‘yan sanda da ke bakin aiki da kuma wani soja da ya zo guttawa a babur a titin Ugwuachara.

Kara karanta wannan

"Allah Yana kallon ka" Babban Malami a Najeriya ya aika saƙo ga Shugaba Tinubu

Taswirar jihar Ebonyi.
Rigimar ƴan sanda da soja ta yi ajalin mutum ɗaya a jihar Ebonyi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ganau ya shaidawa Channels tv cewa ƴan sanda na kan aikin binciken ababen hawa a kan titin amma sojan ya kafe cewa babu wanda zai bincike shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan sanda da soja suka yi arangama

Ya ce sojan ya ki yarda a bincike shi, su kuma ‘yan sandan na kokarin kwace babur din da ya taho a kai.

Garin haka ne faɗa ya kaure tsakanin soja da ƴan sandan har ta kai ga harbe wani ɗan kallo da ke tsaye a gefe tare da jikkata wasu mutane uku.

Kwamishiniyar rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, CP Anthonia Uche-Anya, ta tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Ƴan sanda sun ɗauki mataki kan lamarin

Ta ce a halin yanzu suna tsare da ƴan sandan da kuma sojan, yayin da aka fara gudanar da bincike don gano asalin rikicin.

CP Anthonia ta ce:

"Wasu ƴan sanda ne da ke aikin binciken ababen hawa, suka tsayar da soja, suka nemi bincikarsa shi kuma ya ce sam ba za ta saɓu ba, nan dai rigima ta kaure.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata kan kisan sojoji a jiharsa, ya fadi matakin dauka

"Sojan na kokarin kwance bindigar daya daga cikin jami’an ‘yan sandan ne harsashi ya fita ya sami wani ɗan kallo, ba wai da gangan aka harbe shi ba.

CP ta ƙara da cewa tuni aka kai waɗanda suka ji rauni asibiti don kula da lafiyarsu, gawar wanda aka kashe kuma an ajiye ta a ɗakin ajiyar gawa.

Yan bindiga sun farmaki ƴan sanda a Abia

Kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an ƴan sanda a jihar Abia da ke yankin Kudu maso Gabas.

Ƴan bindigan sun farmaki ƴan sandan ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamban 2024 a ƙaramar hukumar Ohafia ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262