Matasa Sun yi wa Kanin Mahaifinsu Duka da Taɓarya, Ya Mutu har Lahira
- Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta kama wasu matasa bisa zargin kashe kanin mahaifinsu bayan sun masa duka da taɓarya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar yan sanda ta zargi matasan da yi wa kanin mahaifinsu sata bayan masa kisan gilla
- Kwamishinan yan sanda na jihar Bauchi, Auwal Musa Muhammad ya bayyana matakin da za su dauka a kan matasan da ake zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta kama wasu matasa da suka lakaɗawa kanin mahaifinsu duka har ya mutu.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun kashe kanin mahaifin na su ne mai suna Ezekiel Sama'ila dan shekaru 45 bisa zargin maita.
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun kashe kanin mahaifinsu
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu matasa biyu bisa zargin kashe kanin mahaifinsu da suke zargi maye ne kuma ya cinye mutane da dama.
Ezekiel Simon da Lumana Zakka sun kashe kanin mahaifinsu, Ezekiel Sama'ila a karamar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi.
Yadda aka kashe Ezekiel Sama'ila
Bayan an fara neman Ezekiel Sama'ila a ranar 24 ga Satumba ba a same shi ba, yan sanda suka fara bincike.
A yayin bincike aka kama Ezekiel Simon wanda kuma ya tabbatar da cewa sun kashe kanin mahaifinsu ne bayan sun masa duka da taɓarya.
Bayan kashe Ezekiel Sama'ila, matasan sun sace masa wayar hannu da babur da suka sayar N400,000.
Maganar rundunar yan sanda
Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya tabbatar da cewa za a gurfanar da matasan a gaban kotu bayan bincike.
CP Auwal Musa Muhammad ya yi kira ga al'umma da su rika bayar da bayanai ga yan sanda domin cigaba da kama miyagu.
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da aukuwar mummunan al'amari a Masaba da ke karamar hukumar Bursari.
An ruwaito cewa wani matashi mai suna Mai Goni dan shekaru 20 a duniya ya halaka mahaifinsa mai suna Goni Kawu har lahira da tabarya.
Asali: Legit.ng