Kisan kai: Wani daraktan fim da maigadi sun shiga hannun hukuma
Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta damke wani daraktan masana'antar Nollywood mai suna Nonso Ekene tare da wani maigadi mai suna Isaac Sunday, a kan zarginsu da ake yi da kisan wata mata mai shekaru 36 mai suna Obaigeli Onekanse.
Mamaciyar 'yar asalin yankin Ukwu-Nzu ce da ke karamar hukumar Aniocha ta arewa ta jihar. An gano cewa tana zama ne a gida mai lamba 4 da ke titin Anane a kusa da babbar kotun jihar a Asaba.
Kafin rasuwarta, ta kasance mai tsarawa tare da kawata wuraren taro. Hankali ya tashi a makon da ya gabata bayan wani wanda ya santa ya ga mai gadin da motarta bayan bacewarta a wani gidan mai.
A yayin zantawa da manema labarai a kan wannan cigaban, Sirki, Ubangidan maigadin ya bayyana cewa da gaggawa ya iso gidan man inda ya ga Sunday da motar budurwar tare da kayanta a ciki.
Babu kakkautawa kuwa ya sanar da 'yan sanda wadanda suka garzayo har suka kama Isaac Sunday.
Ya ce a yayin binciken, 'yan sandan basu samu komai ba duk da ziyarar da suka dinga kai wa gidan mamaciyar har sai zuwa jiya. Sun lura da wani wuri da suke zargin kabari ne.
Ya ce 'yan sandan sun hake kabarin inda suka samo gangar jikin budurwar da ke rubewa, amma da fuska a kasa tare da hannuwa da kafafu a daure. Sun ga yanka a wuyanta tare da miyagun raunika a sassan jikinta.
KU KARANTA: Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da ya yanke wa budurwa nonuwa a otal (Hotuna)
Babban yayan mamaciyar, Sunday Onekanse, ya zargi 'yan sandan da kin kama jarumin da ke da alaka da kisan kan har sai da kwamishinan 'yan sandan jihar, Hafiz Inuwa ya shiga maganar.
A yayin kira a kan adalci game da lamarin, Onekanse ya jaddada cewa dole ne a damke duk wadanda ke da hannu a kisan 'yar uwarsa.
A yayin rubuta wannan rahoton, 'yan sanda na kokarin fito da gawar budurwar daga kabarin da aka saka ta.
Har a halin yanzu, ba a samu tattaunawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar ba don ba a samun wayarsa.
Amma kuma, wani babban dan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya bada labarain yadda jami'ansu suka damke wani mutum a ranar 27 ga watan Augustan 2020.
Ya kara da cewa, wanda ake zargin ya kasa bada takardun motar ko wata shaida da za ta bayyana shine mamallakin motar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng