Zanga Zanga Ta Ɓarke kan Harbin Hadimin Gwamna a Ofishin Ƴan Sanda, Bayanai Sun Fito
- Mambobin OSTMS sun toshe babban titi a Osogbo, sun bukaci a yi wa shugaban hukumar sufuri ta Osun, Wakeel Alowonle adalci
- Rahoto ya yi iƙirarin cewa an harbi shugaban OSTMS a lokacin da yake tsare a hannun ƴan sanda kan zargin mallakar ƙaramar bindiga
- Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na Osun ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya nemi a gudanar da bincike mai tsafta kuma a buɗe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Ma'aikatan hukumar kula da harkokin sufuri ta jihar Osun watau OSTMS sun ɓarke da zanga-zanga a Osogbo yau Laraba, 20 ga watan Nuwamba.
Masu zanga-zaɓgar sun fantsana kan tituna ne domin nuna fushinsu kan harbin shugaban hukumar, Wakeel Nurudeen Alowonle.
The Nation ta tattaro cewa dakarun ƴan sanda na sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane ne ake zargin sun harbi shugaban hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga: An harbi hadimin gwamna
A ranar Litinin da daddare jami'an ‘yan sanda suka kama Alowonle bisa laifin mallakar bindiga da harsasai na ‘yan sandan Najeriya.
Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na Osun ya yi zargin cewa an harbi hadimin gwamnan har ya kusa mutuwa a hannun ƴan sanda.
A cewarsa, jami'an tsaro sun kama Alowonle ne kan laifin da bai taka kara ya karya ba, suka kusa kashe shi a tsare, ya nemi a yi bincike mai tsafta.
Zanga zanga ta barke a jihar Osun
Masu zanga-zangar sun tare babban titin Aregbe Park, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa a Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda reshen jihar Osun kan wannan lamari da ya fara tada jijiyoyin wuya.
Osun: Rikici ya ɓarke tsakanin sarakuna
A wani rahoton, an ji cewa rigima ta kaure tsakanin wasu sarakunan gargajiya a jihar Osun a game da kauyukan da ke karakashin masarautunsu
Rahotanni sun bayyana cewa an bukaci Gwamna Ademola Adeleke ya kira zama na musamman domin a warware takaddamar.
Asali: Legit.ng