Ma'aikata Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki a Arewacin Najeriya, Bayanai Sun Fito
- Kungiyar NLC a jihar Zamfara sun yi barazanar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 1 ga watan Disambar 2024
- Shugaban kungiyar, Sani Halliru ya ce matakin ya zama dole saboda jinkirin gwamnatin jihar na fara biyan sabon albashin N70,000
- Ma'aikatan sun ba gwamnatin Zamfara wa'adin fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin zuwa karshen watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Kungiyar kwadago ta NLC reshen Zamfara ta bukaci gwamnatin jihar da ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi zuwa karshen Nuwamba.
NLC ta ba gwamnati wa'adin ne a yayin taron majalisar zartarwarta ta jiha (SEC) da ya hudan a Labour House, Gada Biyu, birnin Gusau.
NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki
Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa kungiyar ta yi bazaranar tsunduma yajin aiki a fadin Zamfara muddin gwamnati ba ta aiwatar da sabon albashin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata takarda dauke da sa hannun shugabanta na Zamfara, Sani Halliru, NLC ta nemi gwamnatin jihar ta fara biyan albashin N70,000 zuwa karshen Nuwambar.
Kungiyar ta yanke hukuncin cewa:
"Dukkanin kungiyoyin kwadago a jihar Zamfara sun amince da wa'adin da aka debarwa gwamnati na biyan sabon albashin zuwa Nuwamba.
"Gaza aiwatar da sabon albashin zai tilasta NLC da takwarorinta tsunduma yajin aikin Sai baba ta gani daga 1 ga Disambar 2024."
Zamfara ta amsa kiran NLC ta kasa
Sanarwar Sani Halliru ta ce matakin da suka dauke ya yi daidai da umarnin da NLC ta kasa ta bayar bayan taron NEC a Fatakwal, jihar Ribas, inji rahoton Independent.
NLC ta ce matakin jan ƙafar da wasu gwamnonin jihohi ke yi na fara biyan sabon albashin ya nuna ba sa jin tausayin ma’aikata a wannan lokaci da tsadar rayuwa.
Zamfara: Gwamna zai biya N70,000
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin Zamfara ta sanar da amincewa da Naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.
Gwamnatin ta hannun shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Ahmad Liman, ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Asali: Legit.ng