Fitaccen Attajiri a Najeriya Ya Rasu? An Samu Bayanai kan Gaskiyar Mutuwar Adenuga

Fitaccen Attajiri a Najeriya Ya Rasu? An Samu Bayanai kan Gaskiyar Mutuwar Adenuga

  • Aminin attajiri na biyar a Nahiyar Afrika, Mike Adenuga mai suna Dele Momodu ya karyata labarin da ake yadawa cewa abokinsa ya rasu
  • Momodu ya ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya kan labarin da ake yadawa kan Adenuga inda ya ce a lokacin ma yana cikin aiki
  • Wannan martani na zuwa ne bayan yada cewa Adenuga ya rasu yana da shekaru 71 a duniya a daren jiya Talata 19 ga watan Nuwambar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - A daren jiya Talata 19 ga watan Nuwambar 2024 aka yi ta yada labarin mutuwar attajiri na biyu a Najeriya, Mike Adenuga.

Sai dai na kusa da shi kuma jigon PDP, Dele Momodu ya karyata labarin inda ya ce mai kamfanin GLO da Conoil yana cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Hattara yan TikTok: An daure matashi a gidan kaso kan zagin shugaban kasa

An samu labarin gaskiyar rasuwar attajiri Adenuga
An karyata labarin rasuwar attajiri a Najeriya, Mike Adenuga. Hoto: Icon Sport.
Asali: Getty Images

Jigon PDP ya magantu kan jita-jitar mutuwar Adenuga

Momodu ya fayyace gaskiyar labarin ne a jiya Talata 19 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon PDP ya ce attajirin dan asalin jihar Oyo a lokacin da ake yada labarin yana kan kujera a ofishinsa yana aiki.

Martanin ya biyo bayan yada jita-jitar cewa Mike Adenuga ya rasu yana da shekaru 71 a duniya a daren jiya Talata.

Attajiri Adenuga ya yi godiya ga al'umma

"Ku yi watsi da labarin karya da ake yadawa, jarumi a Afirka, Dr. Michael Adeniyi Agbolade Isola Adenuga yana nan cikin koshin lafiya."
"A yanzu haka yana cikin aiki ba dare ba rana domin taimakawa wurin inganta tattalin arzikin Najeriya."
"Musamman ya kira ni domin yin godiya ta musamman ga wadanda suka nuna damuwa kan abin da ake yadawa."

Dele Momodu

Adenuga ya doke BUA a masu arziki

Kun ji cewa Attajiri, Mike Adenuga ya dawo matsayinsa a rukunin attajiran Najeriya, ya tabbata a matsayin na biyu a kasar nan.

Kara karanta wannan

'Ta burge ni': Abin da Sheikh Kabiru Gombe ya ce a liyafar auren yar Kwankwaso

Mujallar Forbes ta fitar da jerin masu kudi a shekarar nan ta 2024, Mike Adenuga yana gaban Alhaji Abdul Samad Rabiu.

Mista Mike Adenuga mai Dala biliyan $7.4 ya yi suna da kamfanin sadarwa na Globacom wanda shi ne na uku a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.