'Yan Sanda Sun Cafke 'Dan Kasar Waje Mai Safarar Makamai zuwa Najeriya

'Yan Sanda Sun Cafke 'Dan Kasar Waje Mai Safarar Makamai zuwa Najeriya

  • Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar cafke wani ɗan ƙasar waje mai safarar makamai zuwa cikin Najeriya
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana cewa wanda ake zargin ɗan ƙasar Algeria, ya shafe shekara takwas yana shigo da makamai cikin ƙasar nan
  • Mohammed Dalijan ya bayyana cewa an samu nasarar cafƙe wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wani dan ƙasar Algeria mai shekaru 58 bisa zargin safarar makamai ta kan iyaka.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Dalijan ne ya bayyana hakan a birnin Gusau ranar Talata.

'Yan sanda sun cafke mai safarar makamai a Zamfara
'Yan sanda sun cafke dan kasar Algeria mai safarar makamai Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan sanda sun cafke mai safarar makamai

Ya ce ƴan sandan sun ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda 16, a samame daban-daban da suka kai cikin makonni uku da suka gabata, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ƴan sandan ya ce rundunar ta kuma samu nasarar ƙwato makamai a hannun wani da ake zargi da ke ƙera makamai a Jos, jihar Plateau.

Yadda aka cafke waɗanda ake zargi

"Rundunar ƴan sanda, ta hanyar amfani da bayanan sirri ta gano tare da kama wani mai ƙera makamai a Jos, ta bi diddigi tare da cafke wani mai safarar makamai daga Algeria a kan iyakar Illela."
"Wanda ake zargin ɗan kasar Algeria, ya shaidawa ƴan sanda cewa ya shafe shekaru takwas yana aikata wannan laifin."
"Wanda ake zargin yana kai makamai da alburusai ga ƴan bindiga a duk sassan jihohin yankin Arewa maso Yamma."
"A yayin cafke shi, an ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda hudu daga hannunsa."

- Mohammed Dalijan

Mohammed Dalijan ya ce rundunar ƴan sandan ta kuma tsare wasu da ake zargi da suka haɗa da masu sayar da babura ga ƴan bindiga, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mace 'yar fashi da makami da wasu matasa a Bauchi

Ƴan sanda sun ƙi karɓar cin hanci

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Legas sun yi ikirarin sun yi watsi da tayin cin hanci daga wajen ‘dan damfara.

Jami'an ƴan sandan sun bayyana cewa wani da ake zargi da laifin damfara ta yanar gizo, Patrick Akpoguma, ya nemi toshe musu baki ta hanyar ba su rashawar N174m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng