Gwamnatin Kano na Shirin Cika Alkawari, an Fara Runtumo Gagarumin Aiki a Bangaren Ilimi

Gwamnatin Kano na Shirin Cika Alkawari, an Fara Runtumo Gagarumin Aiki a Bangaren Ilimi

  • Gwamnatin Kano ta fara kokarin inganta yanayin koyo da koyarwa a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar
  • Kwamishinan ilimi, Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa an fara gina sababbin ajujuwa 1000 a fadin jihar
  • Wannan wani bangare ne ya cika alkawarin inganta ilimi bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa wa sashen dokar ta baci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauko hanyar cika alkawarin da ta dauka na inganta ilimin mazauna jihar Kano.

Matakin na zuwa bayan gwamnati ta ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi, wanda ta ce ta same shi a cikin mummunan yanayi.

Gwamna
Gwamnatin Abba za ta gina sababbin ajujuwa 1000 a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Arise Television ta wallafa cewa yanzu haka an fara gina ajujuwa 1000 domin rage cunkosin dalibai a ajujuwan da ke makarantun jihar.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya jagoranci maka Wike a kotu kan wulakanta yan Arewa a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a gina ajujuwan karatu a Kano

Watanni shida bayan gwamnati ta tabbatar da dokar ta baci a harkar ilimi, an fara gina ajujuwa 1000 a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Kwamishinan ilimi, Umar Doguwa ne ya bayar da tabbacin, wanda ke ganin rage cunkosu zai kara fadada ilimi da samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa.

‘Ilimi zai inganta a Kano,” Mai sharhi

A karin bayanin da ta yi wa Legit, wani mai sharhi kan ilimi a Kano, Dr. Dan Lami Bala Gwammaja ya ce dama dalibai da dama, musamman na karkara na zaune ne a karkashin bishiya.

A cewarsa:

"Da za a gama ajujuwan kafin sanyi ya kare, kin ga zai taimaka sosai wajen koyo da koyarwa. Uwa uba idan damuna ta zo, wannan yunkuri zai inganta harkar ilimi musamman a karkara.

Ya shawarci gwamnati da ta cigaba da kokarin inganta ilimi tun daga tushe domin amfanin jihar a nan gaba.

Kara karanta wannan

'Kisan mutane 17': Gwamna a Arewa ya hana Fulani daukar fansa bayan harin Lakurawa

Gwamnatin Kano ta fara inganta ilimi

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta ce bangaren ilimi a jihar ya na bukatar kulawa ta musamman ganin mugun yanayin da aka samu koyo da koyarwa a kananan hukumomi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa wasu daga cikin manyan matsalolin da ilimi ke fuskanta sun hada da rashin kwararrun malamai da ingantattun kayan koyo da koyarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.