Yaki Zai Koma Baya: Ana Lallaɓa Tinubu Ya Saki Kasurgumin Dan Ta'adda

Yaki Zai Koma Baya: Ana Lallaɓa Tinubu Ya Saki Kasurgumin Dan Ta'adda

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi magana kan sakin ƙasurgumin ɗan ta'addar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da aka kama a shekarar 2021
  • Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio kan rokon Bola Tinubu ya saki Nnamdi Kanu
  • Sanata Okorocha ya yi rokon ne yayin bikin bankwana da gawar marigayi Sanata Ifeanyi Uba a birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An fara ƙoƙari domin tunkarar shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saki dan ta'addar IPOB, Nnamdi Kanu.

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Rochas Okorocha ne ya buƙaci shugaban majalisar dattawa ya tunkari Tinubu da buƙatar.

Tinubu
Za a roki Tinubu ya saki Nnamdi Kanu. Hoto: Bayo Onanuga| Radio Biafra
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Rochas Okorocha ya fadi haka ne yayin bikin bankwana da Sanata Ifeanyi Uba a Abuja.

Kara karanta wannan

Ifeanyi Ubah: Ndume na son a jawo matar marigayin Sanata zuwa majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a roki Tinubu ya saki ɗan ta'adda

Punch ta wallafa cewa Sanata Rochas Okorocha ya bukaci a roki Bola Tinubu ya saki Nnamdi Kanu domin karrama Ifeanyi Uba.

Okorocha ya ce za a karrama Sanata Ifeanyi Uba ne domin ya sha rokon gwamnati ta saki Kanu amma har ya mutu bai samun hakan ba.

Tun a shekarar 2021 aka cafke dan ta'addar a kasar Kenya aka taho da shi Najeriya kuma daga nan ya fara fuskantar shari'a.

"Ina kira a gare ka ya kai dan uwa na Sanata Godswill Akpabio, ka isar da sako na ga shugaba Tinubu a madadin yan kabilar Ibo.
Hanya mafi kyau da shugaban kasa zai karrama Sanata Ifeanyi Uba ita ce sakin Nnamdi Kanu.
Muna fata idan aka saki Nnamdi Kanu, yan kabilar Ibo za su koma gida su daidaita lamuransu."

- Sanata Rochas Okorocha

Cikin raha, Rochas Okorocha ya ce idan Sanata Akpabio bai isar da sakon ga Bola Tinubu ba zai bi ta hannun matarsa tunda ita yar kabilar Ibo ce.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya jero mutane ya musu godiya bayan auren yarsa

Yayin da yake martani, Sanata Akpabio ya ce bai dauki zancen da wasa ba musamman da ake ce za a saka matarsa a ciki.

DSS ta karyata sakin Nnamdi Kanu

A wani rahoton, kun ji cewa wani rahoto ya ƙaryata iƙirarin cewa an saki Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara.

Wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna wata mata tana bayar da bayanai kan batun sakin Nnamdi Kanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng