Gwamna Ya kai Ziyarar ba Zata a Ma'aikatar Haraji, Bayanai Sun Fito
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar ba zata ma'aikatar tattara haraji domin duba yadda ayyuka ke gudana
- A yayin ziyarar, gwamna Dikko Radda ya samu tarba daga shugabannin hukumar tattara haraji ta jihar da suka hada da Kabiru Isa Fago
- Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa ziyarar na cikin ƙoƙarin ga gwamna Dikko Radda ke yi a jihar domin karfafa gwiwar ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar ba zata ma'aikatar tattara haraji ta jihar Katsina a ranar Talata.
Daraktan ma'aikatar haraji a jihar Katsina, Alhaji Kabir Isa Fago na cikin waɗanda suka tarbi gwamna Dikko Radda.
Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dikko Radda ya kai ziyarar ba zata
Gwamna Dikko Umaru Radda ya kai wata ziyarar ba zata ma'aikatar tattara haraji domin duba yadda ayyuka ke tafiya.
A yammacin ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba gwamnan ya ziyarci ma'aikatar tare da wata tawagar jami'an gwamnati.
Manyan jami'an hukumar tattara haraji da suka hada da daraktoci ne suka tarbi gwamnan yayin ziyarar.
"Gwamna Dikko Radda ya zagaya dukkan ofis ofis da muhimman wuraren ayyuka a ma'aikatar.
Ya kuma duba yadda suke aiki tare da lura da ƙoƙarin da ma'aikata ke yi wajen sauke nauyin da aka daura musu."
- Ibrahim Kaulaha Muhammad
Gwamnatin Katsina ta ce ziyarar na cikin kokarin gwamna Radda na karfafa ma'aikatan gwamnati a fadin jihar.
A karshe, gwamnan ya rubuta sunansa a cikin littafin da masu ziyara ke saka bayanai kafin ya fita daga ma'aikatar.
Dikko Radda ya gana da Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa a Daura.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana dalilin kai ziyarar ga shugaba Muhammadu Buhari kwanaki bayan dawowarsa daga kasar waje.
Asali: Legit.ng