'Kisan Mutane 17': Gwamna a Arewa Ya Hana Fulani Daukar Fansa bayan Harin Lakurawa
- Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya ziyarci al'ummar Fulani da aka kaiwa harin ramuwar gayya a yankin Mera
- Gwamna Nasir Idris ya gargadi Fulanin a kan su guji kai harin daukar fansa kan abin da aka aikata masu a makon da ya gabata
- A ziyarar jajen da ya kai masu, gwamnan ya ba al'ummar Fulanin tallafin N10m tare da alwashin kare su daga barazana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya ziyarci kauyen Mera da ke karamar hukumar Augie domin jajantawa al'ummar garin kan harin Lakurawa.
Legit Hausa ta rahoto cewa wasu da ake zargin 'yan ta'addar Lakurawa ne sun kashe mutane 17 a harin da suka kai kauyen Mera.
TVC News ta rahoto cewa bayan wannan harin ne, wasu mutane suka kai farmaki wata rugar Fulani da ke kauyukan makota.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya hana Fulani daukar fansa
A yayin ziyarar da gwamnan ya kai Mera ranar Talata, ya gargadi mutane a kan kai farmakin daukar fansa yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunta ba.
"Hare-haren daukar fansa na kai ga mutuwar yara, mata da kuma tsofaffi. Ko a lokacin yakin duniya, dokar kasa da kasa ta hana kashe yara, mata da dattawa."
- A cewar gwamnan.
Gwamna Nasir Idris ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kare dukiyoyi da rayukan al'umma tare da yin alkawarin sayo karin motocin sintiri ga jami'an tsaron jihar.
Gwamna ya ba Fulani tallafin N10m
Da ya ke jawabi ga al'ummar Fulani a fadar hakimin Augie, Alhaji Samaila Lamnen-augie, The Punch ta rahoto gwamnan na cewa:
"Gwamnati za ta tabbatar an cafke wadanda suka kai wannan harin daukar fansar. Abin bakin ciki ne yadda wasu suka yi amfani da damar wajen satar kayan jama'a."
Gwamna ya tabbatarwa Fulanin cewa za a basu kariya, inda ya kara da cewa su ma al'ummar Najeriya ne, don haka, dole a kare rayuka da dukiyoyinsu.
Gwamna Idris ya kuma ba al'ummar Fulanin talalfin N10m, yayin da ya ce zai aiko masu da kayayyakin tallafin domin rage radadin wannan farmaki.
Fulani sun wanke kansu daga kai hari
Da ya ke jawabi a madadin al'ummar Fulanin, wani da harin ya shafa, Rugga Hor-e-Mera, ya ce mutane uku daga iyalansa aka kashe, wasu na kwance asibiti.
Ya ce a farmakin da aka kai masu, an kona masu bukkoki 183, sannan an kona amfanin gona da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.
Da yake wanke Fulani daga harin da aka kai garin Mera, Rugga ya ce shi ma ya fuskanci ta'addancin 'yan bindiga a bara, inda suka tafi da shanunsa 80.
Lakurawa sun kashe mutum 5 a Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa yi artabu tsakanin mazauna jihar Kebbi da kungiyar 'yan ta’addar Lakurawa da ta fara bayyana kanta a jihar Kebbi.
An ce an kashe mutane 15 a kazamin fadan da aka yi a lokacin da mayakan Lakurawa suka kai hari kauyen Mera da ke karamar hukumar Augie.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng