Sankara: Mijin Tasleem Ya Bayyana Matsayarsa kan Wanke Kwamishinan Jigawa

Sankara: Mijin Tasleem Ya Bayyana Matsayarsa kan Wanke Kwamishinan Jigawa

  • Nasiru Buba ya nuna rashin gamsuwarsa kan hukuncin da kotu ta yanke na wanke Auwal Sankara daga zargin lalata da matar aure
  • Mijin na Tasleem ya yi watsi da hukuncin kotun shari'ar Musuluncin na wanke kwamishinan ayyuka na musamman na Jigawa daga zargi
  • Nasiru Buba ya bayyana cewa ya gabatar da ƙwararan hujjoji waɗanda za su tabbatar da zargin da yake yi a kan kwamishinan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Nasiru Buba, mutumin da ya zargi kwamishinan ayyuka na musamman na Jigawa, Auwal Danladi Sankara, da yin lalata da matarsa, ya yi martani kan hukuncin kotu.

Nasiru Buba ya yi watsi da hukuncin da kotun shari’ar Musulunci ta yanke na wanke ɗan siyasar daga zargin yin lalata da matarsa.

Mijin Tasleem ya yi watsi da hukuncin kotu
Nasiru Buba bai gamsu da wanke Auwal Danladi Sankara ba Hoto: Auwal D. Sankara
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce da yake tattaunawa da ƴan jarida a birnin Kano, ya nuna rashin gamsuwarsa kan hukuncin da kotun ta yanke.

Kara karanta wannan

Sankara: Kotu ta yi hukunci kan kwamishinan da ake zargi da lalata da matar aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasiru Buba ya bayyana cewa ya gabatar da hujjoji masu yawa domin tabbatar da zargin da yake yi.

Wata kotun shari’ar Musulunci a Kano dai ta yi watsi da ƙarar da aka shigar da Sankara, inda ta ce babu hujjojin da za su tabbatar da zargin da ake masa.

Buba ya ce ya gabatarwa ƴan sanda ƙwararan hujjoji da suka haɗa da hotuna 854, bidiyoyi sama da 100, saƙonnin sautin murya sama da 200 na WhatsApp da kuma bayanan kiran waya na sama da sa’o’i 500.

"Mafi yawan hujjojin na samu ta hannun matata, Tasleem. Idan kotu ta wanke su, ba a wanke su a gaban Allah da idon mutanen da suka san gaskiyar lamarin ba."
"Na bar wa Allah komai kuma shi ne zai yi hukunci Insha Allahu."

- Nasiru Buba

Gwamna ya dawo da Sankara bakin aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar A. Namadi ya dawo da kwamishinan da aka dakatar saboda zargin yin lalata da matar aure

Kara karanta wannan

Durkusar da Arewa: Sabon Ministan Tinubu ya yi wa Kwankwaso martani, ya gargade shi

Gwamna Umar Namadi dai ya dakatar da kwamishinan ne saboda a samu damar masa bincike yadda ya kamata kan zargin keta haddin aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng