Dubu Ta Cika: Sojoji Najeriya Sun Kama Wani Alhaji da Ke Taimakawa Ƴan Bindiga
- Sojoji sun damke wani mutumi ɗan shekara 73, Alhaji Buba Maru, bisa zargin taimakawa ƴan bindiga da bayanai a jihar Taraba
- Dakarun rundunar sojoji ta cafke mutumin ne a lokacin da suka fita kai samamen tsaftace wasu yankuna daga ayyukan ƴan bindiga
- A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce dakarun sun samu nasarar tarwatsa sansanonin miyagu da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Dakarun rundunar birged ta 6 sun cafke wani Alhaji da ake zargin yana taimakawa ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba.
Sojoji sun damke mutumin ne yayin da suka kai samamen tsaftace yankin daga miyagu musamman saboda zuwan lokacin kaka da mutane ke kawo amfanin gona gida.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojojin, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kama wani Alhaji a Taraba
Ya ce sojojin sun maida hankali ne kan fitattun wuraren da ƴan bindiga suka fi zama irinsu tsaunin Bakin Dutse da Sunkani da wasu sansanonin ƴan fashin.
"Sojojin sun yi nasarar tarwatsa manyan sansanonin ƴan bindiga kuma sun cafke wani imfoma da ke taimakawa ƴan ta'addan mai suna Alhaji Buba Maru.
"Mutumin da ya fito ne daga kauyen Bakin Dutse, an ce shi ke ba ƴan bindiga gonakin da suke aikata munanan ayyukansu."
Taraba: Sojoji sun tarwatsa mafakar miyagu
Kyaftin Olibodunde ya kara da cewa sojojin ba su tsaya iya nan, sun faɗaɗa kai hare-hare maɓoyar miyagu har yankin kananan hukumomin Yorro da Zing duk a Taraba.
Ya ce dakarun sun kara samun nasarar tarwatsa wuraren da ake zargin ƴan bindiga na ɓuya.
A nasa bangaren, kwamandan rundunar Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya jaddada kudirin sojoji na tsaftace Taraba daga ayyukan ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da masu garkuwa.
Ya ce sojojin sun yi wannan aiki ne domin tabbatar da manoma sun girbe amfanin gona cikin kwanciyar hankali.
Sojoji sun murkushe ƴan bindiga a Katsina
Ku na da labarin cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga a Katsina a wani hari da suka kai a maɓoyarsu.
Gwarazan sojojin sun hallaka ƴan bindiga 15 a harin wanda suka kai a ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng