'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Hallaka Jami'ai Masu Yawa

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Hallaka Jami'ai Masu Yawa

  • Ana tsoron cewa an samu asarar rayukan jami'an sojojin Najeriya bayan ƴan ta'adda sun farmaki sansaninsu a jihar Borno
  • Ƴan ta'addan waɗanda ake zargin na Boko Haram ne sun hallaka sojoji masu yawa tare da kwashe makamai daga sansanin
  • Gwamnatin jihar Borno ta yi ta'aziyya ga rundunar sojojin Najeriya kan asarar rayukan jami'an da aka samu sakamakon harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Wasu ƴan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai farmaki kan sansanin sojoji a jihar Borno.

Harin na ƴan ta'addan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji masu yawa tare da asarar kayan aikinsu.

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan sansanin sojoji a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan Boko Haram sun farmaki sojoji

Majiyoyi daga ɓangaren sojoji sun shaidawa tashar Channels tv cewa mayaƙan sun kai harin a sansanin da ke garin Kareto a jihar Borno a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke kwamandan 'yan ta'adda da wasu 114

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko da yake babu wani tabbaci a hukumance na adadin waɗanda suka mutu, majiyoyi sun ce an kashe sojoji kusan 20.

Sun bayyana cewa sojojin sun yi artabu da mayaƙan waɗanda suka yi amfani da salon harin ƙunar baƙin wake.

Majiyoyin sun nuna cewa mayaƙan sun ƙwace sansanin sannan suka ƙona shi ciki har da ababen hawa 14.

Ƴan ta'addan sun kuma ƙwace motoci huɗu da makamai masu yawa kafin su bar wajen.

Gwamnatin Borno ta yi alhinin rasa sojoji

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Borno ta yi ta'aziyya ga rundunar sojoji kan kisan jami'anta a Kareto.

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na Borno, Usman Tar ya fitar, Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi Allah wadai da harin na ƴan ta'addan.

An dakatar da malami mai salon Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta sanar da cewa za ta mika rahoton wani malamin addinin Musulunci da ake kira da Muhammad Bin Muhammad ga jami'an tsaro.

Gwamnatin ta ce ta dakatar da dukkanin ayyukan malamin yayin da jami'an tsaro za su bincike shi kan zargin da ake yi masa na yaɗa 'aƙidar Boko Haram'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng