Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Kashe Bayin Allah a Jihar Zamfara
- Ƴan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Dayau a karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara ranar Lahadi da ta gabata
- Mazauna kauyen sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun kashe mutum biyar kuma sun ƙona shaguna da kayan abinci a harin
- Har yanzun rundunar ƴan sanda reshen jihar Zamfara ba ta ce uffan ba kan sabon harin da aka yi wa muane illa a Zanfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Tsagerun ƴan bindiga sun hallaka mutum biyar a kauyen Dayau da ke ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda a jihar Zamfara ranar Lahadi da daddare.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun ƙona gawarwakin waɗanda suka kashe da shaguna da rumbunan ajiyar kayayyakin abinci a ƙauyen.
Ƴan bindiga sun kai mugun hari a Zamfara
Wani mazaunin kauyen, Shamsu Dayau ya shaidawa jaridar Premium Times cewa ƴan bindigar sun shafe kusan sa'o'i bakwai suna ɗanyen aikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shamsu ya ce:
"Da farko ƴan ta'addan sun biyo ta hanyar Kungurki a kan babura, sai suka ci karo da yan banga da dakarun askarawa, suka yi musayar wuta kusan sa'a guda, a karshe maharan suka gudu."
A cewarsa, ƴan ta'addan sun sake komawa kauyen ta wata hanyar bayan sun janye daga artabu da dakarun rundunar Asakarawan Zamfara da ƴan banga.
Yadda miyagun ƴan bindiga suka yi ɓarna
Ya kara da cewa, a lokacin da ‘yan ta’addan suka dawo da misalin karfe 10:00 na dare, ‘yan banga da dakarun CPG sun janye sun ɗauka maharan sun tafi kenan.
Shamsu ya ce da zuwa suka kasu guda biyu, wasu daga cikin ƴan bindigar suka budewa mutane wuta kan mai uwa da wabi, wasu kuma suka ƙona shaguna da gidaje.
"Sun ƙona gidaje huɗu tare da mutune biyar da suka kashe, sun ƙona su har suka zama toka, sannan sun ƙona mana shaguna da kayan abinci," in ji shi.
Har kawo yanzu ba a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Zamfara, Yazid Abubakar kan harin ba.
Zamfara: Sojoji sun yi lugude kan ƴan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Gwarazan sojojin sun yi ruwan wuta kan ƴan bindiga a kauyen da ake kira da Babban Kauye na ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar.
Asali: Legit.ng