'Yan Bindiga Sun Sace 'Yar NYSC bayan Sun Tare Hanya, 'Dan Majalisa Ya Yi Martani
- Wata mai yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta faɗa hannun ƴan bindiga bayan sun yi garkuwa da ita a jihar Neja
- Ƴan bindigan sun sace matashiyar ne lokacin da take kan titin hanyar Neja zuwa Onitsha bayan ta dawo daga jihar Kebbi
- Ɗan majalisar dokokin Imo ya koka da cewa ƴan bindigan sun buƙaci a ba su maƙudan kuɗin fansa kafin su saki mai yi wa ƙasa hidiman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata mai yi wa ƙasa hidima (NYSC) a jihar Neja.
Ƴan bindigan sun sace Chiamaka Obi ne a kan hanyar Neja zuwa Onitsha.
Ƴan bindiga sun sace ƴar NYSC a hanya
Chiamaka Obi, wacce ƴar asalin garin Edenta ne a Okwu Etiti, a ƙaramar hukumar Orsu ta jihar Imo, an yi garkuwa da ita ne a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun sace ta ne lokacin da take dawowa daga jihar Kebbi.
An ce an yi garkuwa da Chiamaka ne tare da wasu ƴan gida ɗaya su huɗu, direban motar bas da wasu fasinjoji uku.
Ɗan majalisa ya yi kira ga gwamnati
Da yake mayar da martani kan lamarin a ranar Talata, ɗan majalisar dokokin jihar Imo, Uche Agabige, ya ce masu garkuwa da mutanen suna neman a ba su maƙudan kuɗin fansa kafin su sake ta.
Agabige ya nuna damuwarsa kan lafiyar Chiamaka Obi, yayin da ya buƙaci gwamnatin jihar Imo da ta ƙaddamar da bincike kan lamarin domin cafke waɗanda suka aikata laifin.
Ɗan majalisar ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya magance matsalar sace-sacen mutane da ƴan bindiga a Najeriya.
Ƴan bindiga sun dauke fasinjoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla fasinjoji 22 ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da su a yankin ƙaramar hukumar Kontagora da ke jihar Neja ranar Alhamis da ta shige.
Ƴan bindigan ɗauke da muggan makamai sun tafi da fasinjojin, wadanda ke tafiya a cikin motoci biyar, zuwa dajin da ke kusa.
Asali: Legit.ng