'Sarakuna ba Su Tsoron Gwamnoni,' Sarkin Musulmi Ya Yi wa Tsohon Gwamna Martani

'Sarakuna ba Su Tsoron Gwamnoni,' Sarkin Musulmi Ya Yi wa Tsohon Gwamna Martani

  • Mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Mohammad Abubakar II ya yi martani ga tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu
  • Sarki Sa'ad Abubakar II ya ce ikirarin Babangida Aliyu na cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoni ba gaskiya ba ne
  • Sarkin Musulman ya ce sarakuna na girmama gwamnoni ne kawai amma ba tsoronsu suke ba saboda sun riga su fara mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Mohammad Abubakar II, ya karyata masu cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin Najeriya.

Sa'ad Abubakar II ya ce tun kafin a ba Najeriya 'yanci a shekarar 1960 sarakunan gargajiya ke mulki a kasar nan.

Sarkin Musulmi ya yi magana kan masu cewa sarakuna na tsoron gwamnonin jihohi
Sarkin Musulmi ya ce sarakuna sun fara mulki tun kafin gwamnoni su fara. Hoto: @sultan_ofsokoto
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto shi ya na cewa sarakunan gargajiya sun fi gwamnoni alakar kusa da mutane kuma sun fi su fahimtar halin da kasar ke ciki.

Kara karanta wannan

'Ba za mu zabi bare ba': Yaron Tinubu ya fara fuskantar kalubale daga matasan Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sarakuna ba su tsoron gwamnoni" - Sarkin Musulmi

Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata a taron masu ruwa da tsaki kan ci gaban matasan Arewacin Najeriya, wanda gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya.

Maganar sarkin Musulman martani ce ga kalaman tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin jihohinsu.

A cewar Sarkin Musulman:

“Na ji cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoninsu. Ba haka ba ne, sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoninsu.

"Sarakuna na girmama gwamnoni" Inji Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sa'ad Abubakar II ya ce duk abin da Allah ya kaddara ne ke faruwa, kuma da aka kawo tsari na dimokuradiyya, sarakunan sun karba hannu biyu biyu.

"Saboda dukkaninmu mun sani, kafin a kawo tsarin shugabanci na gwamnoni sarakunan gargajiya ne ke mulkar Najeriya tun 1914."
"Sarakunan gargajiya na girmama gwamnoni ne kawai, suna girmama gwamnoni saboda suna da iko a jihohohin da suke mulka, amma ba wai tsoro ba."

Kara karanta wannan

Kwana 1 da sakon Tinubu, Gwamnoni sun shiga ganawar gaggawa, an samu bayanai

- A cewar sarkin Musulman.

Sarkin Musulmi: "Ku yi wa shugabanni addu'a"

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III na cewa a duk halin da za a tsinci kai, ba ya dacewa a rika tsinewa shugabanni.

Maimakon tsine masu, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce akwai bukatar 'yan kasar su rika sanya shugabanni cikin addu'a da fatan alheri kan shugabancin da suke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.