An Kawo Gawar Marigayi Sanata Majalisa, Shettima da Sanatoci Sun Yi Masa Bankwana
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci bikin bankwana da gawar marigayi Sanata da ya rasu
- An kawo gawar Sanata Ifeanyi Ubah cikin Majalisar Dattawa domin sanatoci su yi masa bankwana a birnin Abuja
- Wannan na zuwa ne bayan mutuwar Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu a Burtaniya a watan Yulin 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta sadaukar da zamanta na yau kan marigayi Sanata Ifeanyi Ubah a birnin Abuja.
Majalisar ta yi hakan ne domin yin bankwana da gawar Sanata Ubah da aka kawo ta harabarta a yau Talata 19 ga watan Nuwambar 2024.
Sanatoci sun yi bankwana da gawar Sanata
Punch ta ce an ajiye gawar marigayi Sanata Ifeanyi Ubah a gaban Majalisar a cikin akwati domin yin bankwana ga Sanatoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya yi shiga ta musamman domin girmama marigayin da jar hula da bakin gilashi.
Har ila yau, shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele shi ma ya yi shiga irin ta gargajiya kamar Akpabio.
A yayin bikin, an ba har wadanda ba sanatoci ba sanar shiga domin yin bankwana da gawar Sanatan da ke wakiltar Anambra ta Kudu.
Shettima da tsohon gwamna sun halarci bikin
An kawata kujerar Sanata Ubah da ke cikin Majalisar da fulawowi da kuma kyalle mai dauke da tutar Najeriya, cewar The Nation.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da tsohon gwamnan Anambra, Chris Ngige.
Sannan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da shugaban APC, Abdullahi Ganduje da tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha su ma sun halarci bikin da aka gudanar a yau.
Sauran sun hada da tsohon sanatan Anambra ta Tsakiya, Uche Ekwunife da matan Akpabio da Sanata Jibrin Barau da sauran manyan yan siyasa.
Sanata Ifeanyi Ubah ya bar duniya
A baya, mun baku labarin cewa rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa Sanata Ifeanyi Ubah ya riga mu gidan gaskiya kwanaki kadan bayan barin Najeriya.
Marigayin dan jam'iyyar APC da ke wakiltar Anambra ta Kudu ya rasu ne a dakin otal da ke birnin Landan a kasar Burtaniya.
Ubah kafin rasuwarsa, ya ba da gudunmawar N71m ga APC a jiharsa a kokarin kwace mulkin jam'iyyar APGA daga Charles Soludo.
Asali: Legit.ng