Bola Tinubu Ya Aika Saƙo ga Majalisar Dattawa kan Sababbin Naɗin da Ya Yi a INEC

Bola Tinubu Ya Aika Saƙo ga Majalisar Dattawa kan Sababbin Naɗin da Ya Yi a INEC

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunayen mutum uku da ya naɗa a matsayin kwamishinonin zaɓe watau REC ga majalisar dattawa
  • Sababbin kwamishinonin zaɓen sun haɗa da Abdulrazak Yusuf wanda zai kuƙa da shiyyar Arewa maso Yamma da Feyijimi Ibiyemi na Ondo
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta saƙon Bola Tinubu a zauren majalisa ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen kwamishinonin hukumar zabe (REC) guda uku ga majalisar dattawan Najeriya domin tantancewa.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta sakon Bola Tinubu a zaman sanatoci na yau Talata, 19 ga watan Nuwamba, 2023.

Akpabio da Tinubu.
Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da naɗin sababbin kwamishinonin zaɓe 3 Hoto: The Nigerian Senate, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya aika saƙo zuwa majalisa

Channels tv ta ruwaito cewa bayan karanta sakon, majalisar ta amince da miƙa wannan buƙata ga kwamitin da ke kula da harkokin hukumar zaɓe ta kasa watau INEC.

Kara karanta wannan

Sanatan NNPP ya samu saɓani da Kwankwaso, ya faɗi shirinsa a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta umarci kwamitin da ya hanzarta gudanar da aikinsa kan sababbin kwamishinonin zaɓen sannan ya dawo da rahoto a lokacin da ya dace.

Sunayen waɗanda Tinubu ya naɗa RECs

Waɗanda shugaban ƙasa Tinubu ya naɗa sun haɗa da Saseyi Feyijimi Ibiyemi a matsayin kwamishinan INEC mai kula da jihar Ondo.

Sai kuma Abdulrazak Yusuf da shugaban ya naɗa a matsayin kwamishinan zaɓe mai kula da shiyyar Arewa Arewa maso Yammacin Najeriya.

Mista Ibiyemi zai maye gurbin marigayi Niyi Ijalayi, wanda Allah ya yi wa rasuwa a birnin Abuja bayan fitowa daga taron da hukumar INEC ta shirya.

INEC ta sa ranar zaɓen gwamna a Anambra

A wani rahoton, an ji cewa hukumar INEC ta bayyana cewa za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke Kudu maso Gabas a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba, 2025

Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja a taron tuntubar juna da jam’iyyun siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262