"A Yi Mana Bayanin Yadda Ake Raba Arzikin Kasa," Gwamnan PDP Ya Taso Tinubu
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bukaci gwamnatin tarayya da ta rika fitar da bayanai kan raba arzikin kasa
- Ya zargi gwamnatin karkashin Bola Tinubu da yi wa yan kasar nan rufa rufa kan yadda ake raba arzikin Najeriya ga jihohi
- Sanata Bala Mohammed ya ce yan Najeriya su na da hakki su san dalilin hana su arzikin mai da kuma gas da ake samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya nemi gwamnatin tarayya da ta yi wa yan Najeriya bayanin kan rashin cin moriyar arzikin da ake samu a bangaren gas da fetur.
Gwamna Bala Mohammed ya ce yan Najeriya ba su samun tallafin mai da iskar gas kamar yadda ake samu a baya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnan ya bayyana cewa dole ne gwamnatin tarayya ta shaidawa yan kasar nan yadda ta ke rarraba dukiyarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Bauchi ya dura kan Bola Tinubu
Gwamnan jihar Bauchi, Bola Mohammed ya yi zargin cewa yan kasar nan sun daina cin moriyar arzikin da ake samu a fannin mai da iskar gas.
Ya shaidawa Ministan tattalin arziki da tsare-tsare, Wale Edun cewa tun bayan da Tinubu ya hau karagar mulkin kasar nan aka daina samun wannan arziki.
Gwamna Bala ya shawarci Tinubu
Gwamnan jihar Bauchi, Bola Mohammed ya shawarci gwamnatin tarayya da ta rika raba arzikin Najeriya yadda kowace jiha za ta samu kasonta.
Ya nemi gwamnati ta tabbatar da cewa ba wai ana samar da fetur din ne kawai domin sayarwa ba, har da rarraba tattalin arziki ga jihohi.va
Gwamnan Bauchi ya gayawa Tinubu gaskiya
A baya mun ruwaito cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya soki jawabin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fada kan masu zanga-zanga a kasar nan.
Sanata Bala Mohammed a shawarci gwamnati ta daina kokarin ba da uzuri kan gazawarta, tare da daukar matakin kakkabe matsalolin da da yan Najeriya su ke fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng