Babu PDP Babu APC: 'Yan Majalisun Arewa Sun Taru Sun Nuna Adawa da Kudirin Tinubu
- Kudirin haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisa ya cigaba da jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma
- Yan majalisar tarayya da suka fito daga Arewacin Najeriya sun bayyana illar da kudirin zai haifar a yankunansu
- Rahotanni sun nuna cewa yan majalisun Arewa daga PDP da APC ne suka nuna rashin gamsuwa da kudirin harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kudirin haraji da shugaba Bola Tinubu ya aika majalisa a watan Satumba ya cigaba da samun suka.
Wasu yan majalisa daga Arewacin Najeriya sun ce sabon tsarin zai cutar da yankinsu idan aka tabbatar da shi.
Shugaban majalisar dokoki, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya wallafa yadda suka zauna domin nazari kan kudirin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan majalisar Arewa sun soki kudirin haraji
A jiya Litinin yan majalisar dokoki suka zauna domin nazari kan kudirin haraji da Bola Tinubu ya aika musu.
Yan majalisa daga Arewacin Najeriya sun nuna fargaba kan illar da kudirin zai jawo a jihohinsu.
Daily Trust ta wallafa cewa Yusuf Adamu Gagdi (APC), Ahmed Jaha Babawo (APC) da Zakariah Dauda Nyampah (PDP) na cikin waɗanda suka soki kudirin.
"An samu rashin tsaro a yankunan Arewacin Najeriya, saboda haka idan aka tabbatar da kudirin za a samu koma baya a kan harajin VAT.
Akwai bukatar sake nazari kan yadda ake so a dawo raba haraji a Najeriya, jihohin da suka samu koma baya a bangaren tattali ba za su samu riba ba."
- Yan majalisun Arewa
Yan majalisun sun bukaci a yi nazarin kudirin ta inda ba za a cutar da wani yanki a Najeriya ba.
Sanata Kawu Sumaila ya ce yan majalisun Arewa za su yi dubi da yadda kudirin zai shafi mutanensu wajen yanke hukunci.
Haraji: Ana yi wa 'yan majalisa barazana
A wani rahoton, kun ji cewa yan majalisun tarayya sun fara fuskantar barazana kan kudirin haraji na shugaba Bola Tinubu.
Hon. Philip Agbese ya bayyana cewa wasu gwamnonin jihohi sun fara barazanar hana duk dan majalisar da ya goyi bayan kudirin takara a 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng