"Jama'a Shaida ne:" Gwamnatin Tinubu Ta Ce Ana Fattakar 'Yan Ta'addan Lakurawa
- Gwamnatin Najeriya ta sake kwantar da hankalin yan kasar nan, musamman na shiyyar Arewa maso Yamma
- Ministan tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana cewa sun samar da manyan makamai don ta'addanci
- Wannan na zuwa ne bayan jama'a sun nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta kashe tasirin Lakurawa kafin su girma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Gwamnatin tarayya ta ce jama'a sun fara ganin ayyukan dakarun sojojin kasar nan wajen korar yan ta'addan Lakurawa daga Najeriya.
Ministan tsaro, Muhammadu Badaru Abubajar ne ya fadi haka bayan kai ziyarar aiki tare da duba kayayyakin yakin jirage na rundunar Operation Fansan Yamma, a Jihar Sakkwato.
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Muhammadu Badaru ya kara da cewa ba iya yan ta'addan Lakurawa sojojin su ka budewa wuta ba, har da sauran yan ta'adda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji su na fatattakar 'yan Lakurawa
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa Ministan tsaro, Muhammadu Badaru Ababukar ya ce sojoji sun fatattaki wasu daga cikin Lakurawa da su ka kai hari Kebbi.
Ya bayyana cewa jama'a da ke zaune a yankunan da sojojin su ka gudanar da ayyukansu shaida ne na yadda zaratan dakarun ke korar yan ta'addan.
Yadda ake korar 'yan ta'addan Lakurawa
Ministan tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin kasar nan ta samar da manyan makamai da za su taimaka wajen yaki da yan ta'adda.
“Mun kaddamar da sababbin makamai a Katsina tare da kaddamar da sabbabbin jiragen yaki masu saukar ungulu domin fatattakar ’yan fashin daji da Lakurawa, kuma za mu sake tura wasunsu zuwa Sakkwato,” a cewar Ministan.
Sojoji sun dura kan Lakurawa
A baya kun ji yadda dakarun sojojin Najeriya su ka fara takure sababbin yan kungiyar ta'addancin Lakurawa, musamman wadanda ke da sansani da ayyukansu a jihar Kebbi.
Dakarun sojan sama da na kasa ne su ka hada hannu wajen ragargazan yan kungiyar Lakurawa tare da tilasta masu ficewa daga jihar, tare da neman mafaka a Kudancin Kwara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng