Bayan Yabon Tinubu a baya, IMF Ta Nuna Manufofin Tattalin Arziki Ba Su Aiki
- Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya yadda manufofin gwamnatin Bola Tinubu ya gaza farfado da tattalin arziki
- A rahoton asusun da mataimakiyar shugabansa, Catherine Patillo ta gabatar a an gano babu Najeriya a kasashe masu cigaba
- Wannan rahoton ya karyata gwamnatin tarayya da ta bayyana cewa manufofinta sun fara farfado da tattalin arzikin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Rahoton asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya fito da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki duk da fara amfani da manufofin Bola Tinubu.
Rahoton na baya-bayan nan wanda aka gabatar a jihar Legas ya nuna cewa Najeriya ba ta cikin kasashen da su ka samu cigaba ta fuskar tattalin arziki.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa har yanzu Najeriya ta na cikin kangi yayin da ake shan wahala duk da kaddamar da manufofin gwamnatin tarayya watanni 18 baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tattalin arzikin Najeriya ya samu koma baya
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tattalin arzikin kasar nan bai kai 3.19% na cigaba da aka sa rai zai zai kai ba, wanda ke nuna gazawar tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnati.
A rahoton da mataimakiyar IMF, Catherine Patillo ta gabatar, ta ce an yi hasashen tattalin arzikin nahiyar Afrika zai kai 3.6% a shekarar 2024, amma kasar nan ba ta kai matakin ba.
Kasashen Afrika sun kere Najeriya cigaba
Kasashen Côte d’Ivoire, Ghana da Zambia na gaba-gaba a cikin wandanda su ka samu cigaban tattalin arziki a bana, kamar yadda rahoton ya bayyana.
IMF ya bayyana cewa Najeriya na fama da wasu kalubale da su ka hada da rashin daidaiton farashin canjin kudi da faduwar darajar Naira.
"Babu ruwanmu cikin matsin Najeriya:" IMF
A baya mun kun ji cewa asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya barranta kansa da halin da Najeriya ta ke ciki da matsin rayuwa da lalacewar tattalin arziki a gwamnatin Tinubu.
Wannan na zuwa ne bayan wasu daga cikin masu sharhi da masana tattalin arziki su ka dora alhakin wahalar da ake sha kan shawarwarin da asusun IMF ya ba gwamnatin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng