‘Mu Rika Uzuri’: Pantami Ya Magantu kan Zuwan Kabiru Gombe Liyafar Aure a Kano

‘Mu Rika Uzuri’: Pantami Ya Magantu kan Zuwan Kabiru Gombe Liyafar Aure a Kano

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya fusata da yadda ake zargin Malamai ba tare da sanin abin da ke zuciyarsu da kuma nufinsu ba
  • Farfesa Pantami yana magana ne kan zuwan Sheikh Kabiru Gombe liyafa a auren yar Sanata Rabiu Kwankwaso a Kano
  • Shehin malamin ya ce ko gidan giya malami ya yi wa'azi ba laifi ba ne saboda fadakarwa ya je yi kuma kowa yana laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan ce-ce-ku-ce da ake yi game da zuwan Sheikh Kabiru Gombe liyafa a auren yar Sanata Rabi'u Kwankwaso.

Farfesa Isa Pantami ya ce bai kamata al'umma su yanke hukunci kan abin da ke zuciyar dan Adam da ba su sani ba.

Kara karanta wannan

Yadda Musulmi ya sha yabo da ya ba coci kyautar makeken dakin ibada, ya jero dalilai

Farfesa Pantami ya nuna damuwa kan yadda ake munana zato ga malamai
Farfesa Isa Ali Pantami ya shawarci al'umma su rage mummunan zato ga malaman addini. Hoto: Professor Isa Ali Pantami, Karatuttukan Malaman Sunnah.
Asali: Facebook

Pantami ya magantu kan zuwan Kabiru Gombe liyafa

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Pantami ya ce idan aka gayyaci malami ko dakin bautar gunki ne idan ya ga akwai maslaha dole zai je domin fadakarwa.

"An kira malamin addini wa'azi, ba ka san ta yaya aka gayyace shi ba, ba ka san me aka rubuta a takardar gayyatar ba, kawai ka ganshi a wurin taro ka ce kwadayi ya kai shi wurin liyafa ko wa'azi."

- Farfesa Isa Pantami

'Ko dakin bautar gunki malami zai je' - Pantami

"Ka shiga zuciyarsa ka gani ne? kawai ka ce duniya da kwadayi ne ya kai shi wurin wa'azi tabbas zai iya fadar wata kalmar wacce ba ta dace ba, yana iya yiwuwa."
"Shi mai addini idan aka gayyace shi dakin bautan gunki ya yi wa'azi kuma ya fahimci maslaha ne ba zai je ba?"

Kara karanta wannan

'Kowa ya shirya': Malami ya hango gagarumar matsala da ke tunkaro Najeriya a 2025

- Malam Isa Pantami

Malamin ya nuna damuwa kan yadda al'umma ke yanke hukunci kan abin ke cikin zuciyar wanda suke zargi da Allah ne kadai ya sani.

Sheikh Kabiru Gombe ya yaba yar Kwankwaso

Kun ji cewa Sheikh Gombe ya yaba da shigan yar Sanata Rabiu Kwankwaso mai suna Dr. Aisha Rabiu Kwankwaso a yayin liyafar daurin aurenta.

Shehin malamin ya ce shigan amaryar ya yi matukar burge shi inda ya bukaci a yi koyi da irin ita duba da yadda ta rufe jikinta tun daga sama har kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.