Yadda Musulmi Ya Sha Yabo da Ya ba Coci Kyautar Makeken Dakin Ibada, Ya Jero Dalilai
- Wani Musulmi a jihar Oyo ya yi abin a yaba da ya ba cocin St John kyautar makeken dakin taro domin cigaba da ayyukansu
- Musulmin mai suna Ahmed Raji ya ce ya ba da kyautar saboda yadda cocin bai nuna wariya ga sauran addinai da ke yankin Iseyin a Oyo
- Alhaji Raji ya bayyana himmatuwarsa wurin tabbatar da ba da goyon baya da kuma gudunmawa ga cocin a kowane lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Wani Musulmi ya sha ruwan yabo bayan ya ba coci kyautar dakin taro na musamman.
Alhaji Ahmed Raji wanda ya kasance babban lauya ya ba cocin St. John da ke Isalu a Iseyin da ke jihar Oyo kyautar dakin taron domin nuna hadin kai.
Musulmi ya ba coci babbar kyauta ta musamman
The Guardian ta ce Raji ya dauki matakin ba coci kyautar saboda yadda ba su nuna wariya ga sauran addinai musamman Musulmai a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon dakin taron mai wurin zama 400 an sanya masa suna 'Leke Abegunrin' domin maye gurbin tsohon wurin ibada mai shekaru 80 da ya rushe.
Yayin martaninsa, Raji ya bayyana himmatuwarsa wurin ba da gudunmawa ga cocin a kowane lokaci.
Ya yaba da yadda cocin ke ba da gudunmawa a bangaren ilimi da lafiya wanda shi ma ya sauya rayuwarsa gaba daya.
Yadda Raji ya dade yana taimakon coci
A shekarar 2022, Alhaji Raji ya ba wani asibiti da coci ta gina kyauta makamancin wannan inda ya ce asibitin ya taimaka wurin ba al'umma kulawa ta musamman.
Rabaran Gabriel ‘Leke Abegunrin da aka radawa dakin taron sunansa, ya yabawa Alhaji Raji kan irin halayensa na kirki.
An samu zaman lafiya tsakanin Berom da Fulani
A baya, kun ji cewa a jihar Filato, an fara samun zaman lafiya tsakanin kabilun Fulani da Berom da suka shafe shekaru suna fada da juna.
Kungiyar samar da zaman lafiya ta YIAVHA ta shiga ƙauyukan da ake fama da yawan rikici sosai domin sasanta kabilun.
A damunar bana, an samu hadin kai tsakanin Fulani da Berom inda suka yi noma kuma suka hada kai wajen girbe amfanin gona.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng