Shugaba Tinubu Ya Tsige Shugabar PTAD bayan Watanni 13, Ya Ƙara Naɗa Mace
- Bola Ahmed Tinubu ya sauke Dr. Chioma Ejikeme daga matsayin shugabar hukumar fansho ta ƙasa watau PTAD
- Shugaban ƙasar ya kuma maye gurbinta da Miss Tolulope Abiodun Odunaiya ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024
- Mai magana da yawun hukumar PTAD na ƙasa, Olugbenga Ajayi ne ya tabbatar da wannan sauyi da aka samu a wata sanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaba ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tsige Dr. Chioma Ejikeme daga matsayin babbar sakatariya/shugabar hukumar fansho ta PTAD.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun PTAD na ƙasa, Olugbenga Ajayi, ya fitar ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024.
Shugaba Tinubu ya naɗa mace ta jagoranci PTAD
Ya ce shugaban kasar ya nada Miss Tolulope Abiodun Odunaiya a matsayin sabuwar shugabar hukumar fansho, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai bai bayyana ainihin dalilin da ya sa shugaban ƙasa ya tsige Dr. Chioma ba watanni 13 kacal bayan sabunta naɗinta.
Sanarwar ta ce:
"Muna sanar da al'umma musamman ƴan fansho da masu ruwa da tsaki cewa shugaba Bola Tinubu ya naɗa Miss Tolulope Abiodun Odunaiya a matsayin shugabar PTAD.
Sabuwar shugabar PTAD ta kama aiki
Miss Odunaiya ta kama aiki nan take a sabon muƙamin da Tinubu ya naɗa ta yau Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024 a hedikwatar PTAD da ke Abuja.
An ruwaito cewa jagorori da sauran ma'aikata a hukumar fanshon sun tarbi sabuwar shugabarsu da ta fito aiki yau Litinin.
Sanarwar ta ƙara da cewa ta yi ɗan taƙaitaccen jawabi ga ma'aikatan PTAD, inda ta yi alƙawarin ɗorawa daga wurin da magabanta suka tsaya.
Osunaiya ta yi alkawarin jagorantar hukumar bisa tsari da manufofin da aka kafa ta akai wanda ya yi daidai da ajendar shugaban ƙasa ta sabunta fata.
Tinubu ya karawa ƴan fansho albashi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ma'aikatan da suka yi ritaya daga aikin gwamnati za su samu karin kudin fansho da N32,000.
Gwamnatin ta bakin hukumar NSIWC ta ce karin kudin fanshon ya biyo bayan aiwatar da sabon mafi karancin albashi da aka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng