Haraji: Bayan Barazanar Gwamnoni, Majalisa Ta yi Magana kan Buƙatar Tinubu

Haraji: Bayan Barazanar Gwamnoni, Majalisa Ta yi Magana kan Buƙatar Tinubu

  • Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Abbas Tajudeen ya yi magana kan kudirin haraji da shugaba Bola Tinubu ya tura musu
  • Hon. Abbas Tajudeen ya bayyana muhimmancin da yake cikin harkar haraji inda ya ce kowace kasa ta wannar hanyar ta samu cigaba
  • Duk da haka, majalisar dokokin ta ce za ta yi dubi kan buƙatar shugaban kasar idan suka zauna a gobe Talata, 19 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar dokokin Najeriya ta yi magana kan kudirin haraji da Bola Tinubu ya aika mata a watan Satumba.

Kudirin haraji na Bola Tinubu ya haifar da takaddama tsakanin fadar shugaban kasa da gwamnonin jihohi.

Majalisa
Majalisa ta yi magana kan kudirin haraji. House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban majalisa, Abbas Tajudeen ya yi bayani kan kudirin ne a yau Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Yi wa 'Yan Majalisa Barazanar Rasa Takarar 2027 kan Kudirin Harajin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayar majalisa kan kudirin haraji

Daily Post ta wallafa cewa Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Abbas Tajudeen ya ce har yanzu ba su yanke matsaya kan buƙatar shugaba kasa Bola Tinubu ba.

Abbas Tajudeen ya ce sun tattauna a yau Litinin ne domin su samu fahimtar kudirin da matakin da za su dauka a kansa.

Ya kara da cewa zaman da suka yi zai ba yan majalisu damar gano inda ya kamata a yi wa kwaskwarima.

"Zaman da muka yi yau zai taimaka mana wajen sanin inda yake bukatar gyara a cikin kudirin domin mu tabbatar ya dace da tsarin mulkin kasa na 1999.
Tattaunawa kan kudirin haraji na cikin abubuwan da majalisa za ta mayar da hankali a kai saboda alakar da yake da tattalin arziki.
Haraji yana da muhimmanci domin da shi ake amfani wajen ayyukan cigaba a harkar Ilimi, kiwon lafiya da sauransu."

- Abbas Tajudeen

Kara karanta wannan

'Ta burge ni': Abin da Sheikh Kabiru Gombe ya ce a liyafar auren yar Kwankwaso

Yanzu dai kallo ya koma kan yan majalisa domin ganin yadda za su ƙare wajen tattaunawa kan kudirin a gobe Talata.

An yi barazana ga yan majalisa kan haraji

A wani rahoton, kun ji cewa yan majalisa sun fara fuskantar barazana kan amincewa da kudirin haraji na Bola Tinubu.

Hon. Philip Agbese ya ce gwamnonin jihohi sun fara barazanar hana yan majalisa tikitin takara a 2027 idan suka amince da kudirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng