'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Jami'an Tsaro har Lahira
- An yi rashi na jami'an tsaro bayan ƴan bindiga sun kai musu hari a jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
- Ƴan bindigan a hare-haren da suka kai da safiyar ranar Litinin, sun hallaka jami'an tsaro na ƴan banga guda huɗu
- Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ba ta faɗi adadin mutanen da suka rayukansu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a jihar Anambra inda suka kashe jami’an tsaro guda huɗu.
Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a tsakanin ƙarfe 8:00 na safe zuwa ƙarfe 8:45 na safiyar ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamban 2024.
Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Anambra
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa harin farko ya faru a ƙauyen Abatete da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin na ƴan bindigan ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ƴan banga uku da ke tare da shugaban ƙauyen Abatete, Cif Ezebinobi Ezigbo.
Harin na biyu ya faru ne a kwanar Ukpo da ke ƙaramar hukumar Dunukofia da misalin ƙarfe 8:45 na safe inda ƴan bindigan suka hallaka ɗan banga ɗaya tare da ƙona motarsu ƙirar Sienna.
Rahotanni sun ce shugaban ƙauyen Abatete ya samu raunuka a yayin harin.
Wata majiya a Abatete ta ce an garzaya da shugaban zuwa asibiti duk da cewa akwai fargabar da wuya ya rayu.
"Muna fatan ya tsira saboda mun samu labarin cewa harsashi ya same shi a kai."
- Wata majiya
Ƴan sanda sun yi martani bayan harin
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai, kakakin ƴan sandan ya ce ba zai iya tabbatar da adadin mutanen da aka kashe, jikkata ko kuma aka sace ba.
Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Hare-haren da aka kai ta sama a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe ya yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata maɓoyarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng