Bayan Shekaru, Kanal Fadile Ya Fadi Yadda Buhari Ya Nemi Ya Kore Shi daga Gidan Soja
- Lauyan sojoji na farko, Kanal Babatunde Fadile ya fadi yadda tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya so raba shi da aikinsa
- Ya ce sun fara haduwa a garin Ibadan, a lokacin Muhammadu Buhari ya na matsayin mai kula da sojojin kasa da ke Oyo
- Kanal Fadile mai ritaya ya ce shi ya jagoranci rubuta wasikar korafi kan yadda Buhari ya sa aka rufe sojoji da aka kama da laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT Abuja - Wani tsohon soja, Kanal Babatunde Bello Fadile ya fadi yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya so a kore shi daga rundunar kasar nan.
Ya bayyana haka ne ta cikin wani littafinsa mai suna 'Nine Lives: The Bello-Fadile Memoirs,' inda ya ce lamarin ya afku a 1981.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Buhari, wanda ke a matsayin jami'in da ke kula da sojojin kasa, reshen Ibadan a jihar Oyo ya fusata da matakin da Fadile ya dauka.
Yadda Fadile ya gamu da Muhammadu Buhari
Kanal Babatunde Bello Fadile mai ritaya ya bayyana yadda ya fara haduwa da Muhammadu Buhari a lokacin da aka kama wasu sojoji da laifi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kanal Fadile mai ritaya ya ce a lokacin ne Buhari ya sa aka tsare sojojin a wurare mabanbanta, lamarin da ya sa aka rubuta takardar korafi ga babban hafsan soja.
Dalilin Buhari na son korar Fadile
Kanal Babatunde Fadile mai ritaya, lauyan soja na farko a Najeriya ya rubuta wasikar korafi ga babban hafsan soja, Laftanar Janar Mohammed Inuwa Wushishi.
Ya yi zargin Buhari ya sa an tsare wasu sojojin a dakin killace masu laifi ba bisa ka'ida ba, hakan ya fusata Muhammadu Buhari har ya yi barazanar a kore shi ko ya bar aiki.
Kanal Babatunde Fadile mai ritaya ya kara da cewa sai da ya ba Buhari hakuri tare da janye kalmar tsare sojojin ba bisa ka'ida kafin ya tsira daga fushin hukuma.
Buhari ya jajanta rasuwar Lagbaja
A baya mun wallafa cewa tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin tarayya da iyalan hafsan sojojin kasa, Taoreed Lagbaja.
Muhammadu Buhari ya bayyana matukar rashin jin dadin kan babban rashin, tare da mika ta'aziyya ga dukkanin yan Najeriya na rasa jarumin jami'in soja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng