An Rasa Rai da Yan Bindiga Suka Kai Hari kan Yan Sandan da ke Gadin 'Dan Majalisa

An Rasa Rai da Yan Bindiga Suka Kai Hari kan Yan Sandan da ke Gadin 'Dan Majalisa

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Abia na nuni da cewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wasu yan sanda
  • An ruwaito cewa yan sandan na cikin rukunin masu ba da tsaro ga daya daga cikin yan majalisun tarayya da ke wakiltar jihar Abia
  • Karin rahotanni sun tabbatar da cewa miyagu yan bindigar sun kai harin ne bayan sun tare hanya sanye da kayan yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Abia - An yi musayar wuta tsakanin jami'an yan sanda da wasu yan bindiga a daren ranar Lahadi da misalin karfe 9:00.

An ruwaito cewa lamarin ya jawo sanadiyar mutuwar dan sanda da ya yi musayar wuta da miyagu yan bindigar.

Yan sanda
An kashe dan sanda a Abia. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a yankin Ubakala a karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia.

Kara karanta wannan

Ondo: An tarwatsa masu zabe da miyagu suka yi ta harbe harbe, an gano dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai hari kan yan sanda

Wasu miyagu yan bindiga sun sanya kayan yan sanda sun tare hanya a karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia.

Lamarin ya jawo yan bindigar sun tare mota ƙirar Corolla wanda ke dauke da yan sanda biyu da kuma matukin motar.

Da yan bindigar suka gano mutane biyun da ke cikin motar yan sanda ne sai suka fara bude musu wuta nan take.

An kashe dan sanda a jihar Abia

Bayan musayar wuta da yan bindigar, an ruwaito cewa miyagun sun kashe daya daga cikin yan sandan cikin motar.

Haka zalika daya dan sandar ya samu raunuka da ake fargabar da wahala ya yi rai yayin da aka garzaya da shi asibiti.

Yan bindiga sun tsere bayan kisa

A lokacin da yan sandan caji ofis da ke kusa da wajen da abin ya faru suka kai dauki, yan bindigar sun gudu zuwa daji.

Kara karanta wannan

Bayan tsokanar Gwamna, Sanata a Arewa na fuskantar kiranye daga yan mazabarsa

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan sandan da aka kai wa harin suna ba da tsaro ga dan majalisa ne amma ba ya tare da su a lokacin.

Wasu yan bindiga sun kai hari Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun yi rashin imani a jihar Taraba, sun hallaka wani babban manomi da bai san hawa ba bai san sauka ba.

Tsagerun sun kuma yi awon gaba da wasu mamona shida a ƙauyen Garbatau da ke ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng