MTEF: Yadda Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya Za Su Kashe Naira Tiriliyan 6.5 a 2025

MTEF: Yadda Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya Za Su Kashe Naira Tiriliyan 6.5 a 2025

  • Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa kudin da za ta kashe kan albashin ma'aikata za su karu da kashi 60 a shekarar 2025
  • Wannan kari ya samo asali ne daga aiwatar da sabon mafi karancin albashi na kasa da karin albashi ga ma’aikatan tarayyar
  • Karin kaso 60 na nufin cewa albashin ma'aikatan tarayyar zai lakume Naira tiriliyan 6.5 idan aka kwatanta da na shekarar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kudaden da za ta kashe kan albashin ma'aikatanta za su karu da kashi 6 a shekarar 2025.

Ta ce wannan kari ya biyo bayan aiwatar da sabon mafi karancin albashi na kasa da kuma karin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Rahoton MTEF ya nuna cewa albashin ma'aikatan tarayya zai kai N6.5trn a 2025
Gwamnatin tarayya za ta kashe N6.5trn a biyan albashin ma'aikatan tarayya a 2025. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Albashin ma'aikatan tarayya zai lakume N6.5trn

Kara karanta wannan

Dan takarar PDP ya gano babbar matsala a zaben gwamnan Ondo, ya fara sukar INEC

Binciken Punch ya nuna cewa an ware Naira tiriliyan 4.1 a matsayin kudaden albashi a kasafin kudin 2024, wanda karin kashi 60 ke nufin karin Naira tiriliyan 2.46.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce karin kaso 60 na kudin da za a warewa ma'aikatan tarayyar a 2025 na nufin cewa ma'aikatan za su lakume jimillar Naira tiriliyan 6.56.

Wannan bayani ya fito ne daga sabon takardar tsare tsaren kasafin kudin 2025 zuwa 2027 na gwamnatin tarayya (MTEF) da wakilin jaridar ya samu a ranar Lahadi.

Ma'aikatan tarayya sun fara karbar N70,000

Takardar, wadda majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da ita a makon da ya gabata, ta tanadi yadda za a kashe kudaden kasafin shekarun uku.

A watan Yulin 2024, Shugaba Bola Tinubu ya amince da karin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya daga N30,000 zuwa N70,000.

Bincike da ya tabbatar da cewa ma’aikatan tarayya sun fara karɓar sabon albashin amma akwai jihohin da har yanzu ba su fara aiwatar da karin ba.

Kara karanta wannan

Najeriya na tangal tangal, Tinubu zai runtumo sabon bashin Naira tiriliyan 4.2

A cikin rahoton MTEF, gwamnati ta bayyana cewa ya zuwa watan Agusta, ta fitar da Naira tiriliyan 2.67, wanda ya kai kashi 65 na Naira tiriliyan 4.10 da aka ware a kasafin kudin 2024.

Tinubu ya nunka albashin masu shari'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar kara albashi da alawus ga alkalan kasar nan da kashi 300.

Kudurin dokar albashin ma’aikatan shari’ar wanda majalisar dattawa ta amince da shi a watan Yuni, zai bai wa alkalin alkalan Najeriya (CJN) damar samun N64m a duk shekara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.