"Allah Yana Kallon Ka" Babban Malami a Najeriya Ya Aika Saƙo ga Shugaba Tinubu

"Allah Yana Kallon Ka" Babban Malami a Najeriya Ya Aika Saƙo ga Shugaba Tinubu

  • Babban malamin addinin kirista, John Onaiyekan ya ja hankalin Bola Tinubu kan ya tuna Allah ne Ya ba shi mulki kuma Yana kallonsa
  • Onaiyekan ya ce duk da mafi akasarin ƴan Najeriya ba su zaɓi Tinubu ba amma ya zama tilas a kansa ya sauke hakkin kowane ɗan ƙasa
  • Ya tunawa Tinubu cewa akwai ranar da zai kare kansa a gaban Allah kan kujerar mulkin da aka ba shi a nan duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Fitaccen malamin nan, Emeritus Archbishop na Abuja, Cardinal John Onaiyekan, ya bukaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ƴan Najeriya aikin da suke bukata.

Faston ya ce duk da galibin ƴan Najeriya ba su zaɓi Tinubu ba a zaɓen 2023, amma tun da ya zama shugaban kasa, nauyin kowane ɗan ƙasa ya rataya a kansa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya bukaci Tinubu ya kori shugaban INEC Mahmood Yakubu, ya ba da dalili

Cardinal Onaiyekan da Tinubu.
Onaiyekan ya ja hankalin Tinubu kan yadda ya kamata ya tafiyar da mulkin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Babban malamin wanda ke ganin girmansa ya faɗi haka ne cikin shirin ranar Lahadi 'Inside Sources' na gidan talabijin na Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban malami ya ja hankalin shugaba Tinubu

Onaiyekan ya ce kamata ya yi bayan hawa mulki, shugaban ƙasa ya jingine duk wani banbanci siyasa, ya zama shugaban kowa ta yadda zai yiwa kowane ɗan kasa aiki.

Cardinal Onaiyekan ya gargaɗi Tinubu kan nuna wariya wajen naɗin muƙamai da kuma fifita yankin da ya fi samun kuri'u.

Ya ce:

"Ƴan Najeriya da dama ba su dangwalawa APC ba, sai dai ta bayyana cewa APC ta samu mafi rinjayen kuri'u shiyasa a yanzu haka take mulki. Amma mafi yawa ba a zaɓi jam'iyyar ba."
"Ko ma dai me doka ta tanada, a zahirin gaskiya kowa ya san cewa waɗanda ba su zaɓi Tinubu sun fi waɗanda suka zaɓe shi yawa.
"Saboda haka duk da marasa rinjaye suka kafa gwamnatin, ya zama wajibi su ɗauki kowa ɗaya, kuma su ba kowa haƙƙinsa, su shugabanci jama'a da kyau."

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya fadi makomar 'yan ta'addan Lakurawa a Najeriya

"Allah na kallonka" - Onaiyekan ga Tinubu

Cardinal Onaiyekan ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya yi iya bakin ƙoƙarinsa domin zai yi wa Allah bayani filla-filla kan yadda ya shugabanci al'umma

"A matsayin malamin addini, zan iya cewa Allah ne ya baka wannan matsayi kuma idan Allah ya baka mulki ya kamata ka tuna cewa yana nan yana kallonka."
"Kuma ka sani Allah zai tambaye ka abin da ka aikata a wannan mulki da ya ba ka," in ji shi.

Bola Tinubu ya tafi ƙasar Brazil

Kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amsa gayyatar da Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na ƙasar Brazil ya yi masa.

Tinubu ya shilla zuwa birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil domin halartar taron ƙungiyar G20 a ranakun Litinin da Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262