'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Manomi, Sun Sace Wasu Mutane a Arewa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Manomi, Sun Sace Wasu Mutane a Arewa

  • Ƴan bindiga sun yi rashin imani a jihar Taraba, sun hallaka wani babban manomi da bai san hawa ba kuma bai san sauka ba
  • Tsagerun sun kuma yi awon gaba da wasu mamona shida a ƙauyen Garbatau da ke ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba
  • Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ƴan bindiga sun buƙaci a ba su maƙudan kuɗin fansa kafin su saki manoman da suka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Wasu ƴan bindiga sun kashe wani manomi tare da sace wasu manoma shida a Garbatau cikin ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Ƴan bindigan sun kashe manomin mai suna Alhaji Mai Wanda Maibultu a cikin gonarsa a ƙarshen makon jiya.

'Yan bindiga sun kai hari a Taraba
'Yan bindiga sun sace manoma a Taraba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa marigayin babban manomi ne a ƙauyen wanda ke da tazarar kilomita kaɗan daga garin Garba Chede.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban jami'in hukumar NDLEA, an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Taraba

Sauran manoman guda shida an yi garkuwa da su ne a ƙauyen Garbatau, da ke tsakanin wasu tsaunuka biyu.

Wani mazaunin garin Maihula mai suna Adamu Dauda ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan manoman da aka sace inda suka buƙaci a ba su kuɗin fansa Naira miliyan 100.

Adamu ya ci gaba da cewa, a irin wannan lokacin a shekarar da ta gabata ɗaruruwan masu garkuwa da mutane sun mamaye yankin tare da sace manoma da dama, inda suka hana su yin girbin amfanin gonakinsu.

Ya ce manoman suna girbin amfanin gonakinsu amma masu garkuwa da mutane sun dakatar da aikin kamar yadda suka yi a bara.

Ba a samu jin ta bakin 'yan sanda ba

Ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba kuma bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'addanci, sun hallaka tsohon kansila har lahira

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Hare-haren da aka kai ta sama a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, ya yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata maɓoyarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng